Gwamnatin Katsina za ta horas da tubabbun ’yan bindiga dubu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta fara tantance tubabbun ’yan bindiga marasa aikin yi guda 1,000 domin ba su horo kan sana’o’i daban-daban tare da koyar da su ilimin addinin Musulunci.

Shirin na ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Youth Mobilizers for Peace and Progress Forum, tare da haɗin gwiwar Sautus Sunnah Charity Foundation.

Shirin na da nufin bai wa matasan jihar damar samun ilimi da dabarun dogaro da kai, musamman ta hanyar koyar da sana’o’in da za su taimaka wajen samar musu da hanyoyin samun abin dogaro da kai, da kuma rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Sana’o’in da za a koyar da su sun haɗa da fenti, POP, aikin tayal, gyaran waya, gyaran wutar lantarki da sauran sana’o’i.

A yayin tantancewar, ana duba cancantar matasan da za su amfana da shirin kafin a fara ba su horo na musamman, wanda zai haɗa da koyar da sana’o’i da ilimin addini.

Shugaban ƙungiyar, Malam Abdurrahman Hamza Maiyanka, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta aiwatar da irin wannan shiri a baya, inda aka samu nasarori da dama, abin da ya sa aka sake ba da damar tantance ƙarin matasa 1,000 domin su amfana.

Ya ƙara da cewa haɗa koyar da sana’a da ilimin addini zai taimaka wajen gina matasa masu nagarta, ƙwarewa da kishin zaman lafiya, tare da ba su damar taka rawa wajen ci gaban al’umma.

Kazalika, gwamnatin za ta ɗauki nauyin kai matasan zuwa wuraren ayyukansu bayan an kammala tantance su, tare da ɗaukar nauyin ciyar da su sau biyu a rana.

Sauran shugabannin gidauniyar Sautus Sunnah sun yi kira ga matasan da za su amfana da shirin da su yi amfani da damar wajen koyon sana’o’in da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu da kuma zama masu amfani ga al’umma.

Sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen rage yawan matasa marasa aikin yi, tare da bunƙasa sana’o’in hannu, ƙarfafa zaman lafiya da kuma ci gaban al’umma a faɗin Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply