Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An bayyana lokacin Maulidi a matsayin wani lokaci da ake nuna murnar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (SAW).
Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Kayan Doki ta Kasuwar Kurmi, Chiroman Kasuwar Kurmi, kuma Madawakin Alin Mashuwa na Jihar Legas, Alhaji Abba Mai Kayan Doki, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a wajen Maulidin da ƙungiyar ta saba shirya wa duk shekara a Kasuwar Karo na Sha Biyar.
Alhaji Abba ya ce kasancewarsu a wannan hidima da suke shirya wa duk shekara na nuna irin farin ciki da annashuwar da suke ji wajen tunawa da ranar haihuwar Shugaban Halitta.
Ya ce wannan ita ce hanyar da al’umma za su riƙa nuna farin ciki da wannan rana.
Ya kuma yi fatan alheri ga waɗanda suka taimaka wajen tabbatar da gudanar da wannan bikin Maulidi.
Shi ma Sakataren Tsare-tsare na ƙungiyar Masu Sayar da Kayan Doki ta ƙasa, Alhaji Abdullahi Kwamamda, ya ce babban abin da ke ba su ƙarfin gwiwar shirya wannan Maulidi a duk shekara shi ne amfani da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) da ke ƙarfafa sanin Manzon Allah, sanin ahalinsa da kuma karatun Alƙur’ani.
Ya ƙara da cewa tun zamanin da, babu wani abin da ya fi dacewa da al’umma kamar nuna wa ’ya’yansu darajar wannan wata mai albarka na haihuwar Fiyayyen Halitta.
Ya kuma yi kira ga sauran ’yan kasuwa da su riƙa shirya irin wannan Maulidi domin neman albarkar Allah a kasuwancin da suke gudanarwa.
Ya ce ta hanyar irin wannan ne Allah zai riƙa sanya wa sana’arsu albarka da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
A lokacin taron, an naɗa Umar Baban Shehu a matsayin Khadimul Faiza, duba da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban addini da kuma taimaka wa al’umma.
Umar Baban Shehu ya nuna farin ciki da murnar wannan abin da ƙungiyar ta yi masa, yana mai cewa hakan na nuna yadda yake zaune lafiya da al’umma.
Taron Maulidin ya samu halartar manyan malamai, ’yan sha’irai da kuma ƙungiyoyin ’yan kasuwa daga wurare daban-daban.
