2027: Kotu ta umarci a aike wa Tinubu ƙarar Atiku ta neman soke cancantarsa ta shiga takara a hukumance

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a aike wa Shugaba Bola Tinubu ƙarar da ke neman haramta masa shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 acikin mako guda bisa zarge-zargen cewa ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC takardun shaida na bogi.

Mai Shari’a Inyang Ekwo yayin wani hukunci, ya amince da isar da saƙon shari’a ga Shugaba Tinubu ta hannun jam’iyyarsa ta APC. Alƙalin ya bayar da wannan izinin ne bayan sauraren ƙarar da lauyan Atiku, Mista Olanrewaju Omotsyo-OJo ya shigar bayan wakiltar Mista Silas Onu da aka yi wa rashi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027 ne ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026. Yayin da ADC ta zama mai kare ƙara ta biyu, Shugaba Tinubu, APC da INEC sune waɗanda aka shigar ƙara a matsayi na ɗaya, biyu da na uku.

A cikin ƙarar, Atiku ya zargi Tinubu da miƙa wa INEC shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC ta bogi acikin takardun da ya bayar domin neman kujerar shugaban ƙasa. Ya kuma tirje kan cewa, Tinubu ya bayar da bayanan ƙarya akansa a Form mai lamba CF0001 ga INEC, inda ya ankarar da kotun cewa takardar NYSC da ya bai wa hukumar zaɓen tana ɗauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, yana mai cewa “ta wani mai suna Adekunle ce.”

Ya ƙara da cewa, Tinubu ya jima yana amfani da takardar shaidar tun a 1999 a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan Jihar Legas, yana mai kira ga kotun da ta yi amfani da dokar ƙasa da ta hukunta tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa wajen soke cancantar shugaban ƙasar shiga zaɓen na 2027.

Da fari dai kotun ta ayyana 28 ga Satumba a matsayin ranar yanke hukunci kan ƙarar. Tuni dai INEC ta shigar da ƙorafin neman kotun ta yi watsi da ƙarar kan rashin nagarta.

By Babaji

Leave a Reply