2027: Ku sake ba ni dama na ɗora daga inda na tsaya, Tinubu ya roƙi ’yan Nijeriya a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su sake ba shi dama ta hanyar zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar ranar 16 ga Janairun 2027, domin ya samu damar kammala ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ta fara.

Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Talata yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

Ya ce ƙarin wa’adin shekaru huɗu zai ba gwamnatinsa damar ƙarfafa nasarorin da ta samu, tare da kammala ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a sassan Nijeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da hanzarta ci gaba, musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Kebbi cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da Gwamna Nasir Idris domin magance buƙatun jihar na samar da ababen more rayuwa, ciki har da gina sabbin hanyoyi da gyara waɗanda ake da su.

Tinubu ya ce ziyarar tasa Jihar Kebbi ta fi karkata ne wajen gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba shi da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2023.

“Ban zo ne domin yin dogon jawabi ba, na zo ne domin gode muku bisa zaɓen da ya gabata. Kun zaɓe ni, kun zaɓi Kauran Gwandu, kun zaɓi sanatocinmu Adamu Aliero da Yahaya da sauran ’yan takara,” inji shi.

Ya ƙara da cewa goyon bayan da suka ba shi alama ce ta amincewar da suka nuna masa, wadda ya ce zai ci gaba da girmamawa ta hanyar manufofi da shirye-shiryen inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply