2027: Majalisar Wakilai na yin ƙudirin haɗe zaɓukan shugaban ƙasa da gwamnoni rana ɗaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Wakilai ta fara yunƙurin sauya tsarin gudanar da zaɓuka a Nijeriya, yayin da ta ke neman a mayar da yin duka zaɓuka guda biyar da suka haɗa da na shugaban ƙasa, gwamnoni, ƴan majalisar dokoki na tarayya da ƴan majalisun jihohi a rana ɗaya.

Hakan wani yunƙuri ne na yin kwaskwarima ga sabuwar dokar zaɓe ta 2025 da nufin samar da gyare-gyare ga harkokin gudanar da zaɓe a Nijeriya.

Ƙudirin kafa dokar zaɓe a rana guda zai taimaka wajen rage adadin kuɗaɗen da ake kashewa a yayin gudanar da harkokin zaɓuka a faɗin ƙasar, inda a ƙarƙashin haka, za a taƙaice kuɗaɗen da za a riƙa kashewa a zaɓukan kamar haka:

  1. Naira biliyan 10 ga zaɓen shugaban ƙasa, sai biliyan N3 ga zaɓen gwamna.
  2. A zaɓen sanatoci kuwa, Naira miliyan 500 za a riƙa kashewa, sai kuma N250 a na ƴan majalisar wakilai.
  3. Sai Naira miliyan 30 ga na ƴan majalisar jihohi da ciyamomi, yayin da za a riƙa kashe N10m a na kansiloli.

Sai ɓangaren bada tallafin kuɗaɗe ga ƴan takara, inda ƙudirin ke neman a sanya N500m ga kowane ɗan takara domin tabbatar da gaskiya da rage kuɗaɗen siyasa.

A harkokin rajistar jam’iyya kuwa, ƙudirin na neman a sanya miliyan N50 a matsayin kuɗin rajista ga kowace jam’iyya, yayin da za a ci tarar N20m ga duk jam’iyyar da ta ƙi kiyaye dokar ko a tasa ƙeyar jagororinta zuwa kurkuku.

Haka kuma, za a soke gudanar da zaɓen cike gurbi ga kujerun ƴan majalisar dokoki, inda za a nemi jam’iyyar da wanda ke riƙe da kujerar ya ke (idan ya yi murabus ko ya rasu) da ta samar da wanda zai maye gurbinsa cikin kwana 60 ba tare da gudanar da zaɓe ba.

Sannan, jam’iyyu za su miƙa jaddawalin sunayen ƴan takarkarunsu ga INEC kwanaki 210 kafin gudanar da babban zaɓe ciki har da takardun da suka tabbatar da cancantar tsayawar ɗan takara a dokance.

Kazalika, za a koma tantance masu zaɓe ta hanyar gabatar da lambobinsu na QR, ko lambobin ‘National ID’ ko wasu lambobin gabatar da kai da ƙasa ta amince da su ga tsarin tantancewa ta fasahar BVAS ko wanda hukumar zaɓe ta samar.

Bugu da ƙari, manyan malaman zaɓe sai sun tabbatar da adadin masu zaɓe da aka tantance ya yi daidai da rahoton na’urar BVAS da na mazaɓu gabannin sanar da sakamako.

Sauran batutuwan sun haɗa da ƙorafi bayan sanar da sakamakon zaɓe, wanda wajibi ne a shigar kwana 21 bayan haka dai sauransu.

By Babaji