
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban Makarantar Lauyoyi guda shida sun nemi a biya Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa ga kowane ɗaya daga cikin ɗaliban.
A ranar Asabar aka yi garkuwa da ɗaliban, waɗanda suak taho daga garin Onitsa dake jihar Anambara domin zuwa reshen makarantar dake Yola a Jihar Adamawa.
Lamarin ya ayyukan a yankin Wukari dake Jihar Taraba, a titin iyakar Ƙaramar Hukumar da yankin jihar Benuwai.
Ɗaya daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su a wata hira da wani takwaransa, ya ce ana buƙatar N20m a matsayin kuɗin fansa domin sako shi ga hannun ƴan bindigar.
Ɗaliban da ke koka ƴan bindigar sune: Ernest Okafor, Thomas Sankara,
Ogbuka Fabian, Nwamma Philip, Okechukwu Obadiegwu, Obalem Emmanuel da kuma Obiorah David.
Lamarin ya haifar da tsoro acikin al’umma musamman ɗalibai da masana harkar shari’a duab da cewa hakan ba shi ne karo da farko da ake garkuwa da ɗaliban ɓangaren ba.
