
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka wata mata mai ɗauke da juna biyu da wani matashi yayin wani mummunan hari da suka ƙaddamar a ƙauyen Rim da ke Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.
A cewar wasu majiyoyi daga yankin, maharan sun je ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, inda suka buɗe wuta ga jama’a, lamarin da ya yi ajalin mutane biyu tare da jefa mutane cikin firgici.
An bayyana marigayiyar da suna Misis Happiness Pam mai shekaru 32 da kuma Daniel Luka ɗan shekara 24 da suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin.
A cewar wata sanarwa da Ƙungiyar Matasan Al’ummar Birom (BYM) ta fitar da hannu Sakatarenta Mista Rwang Tengwong, ƙungiyar ta samu rahoton faruwar al’amarin cikin alhini da baƙin ciki.
Ta ce, irin wannan na cigaba da faruwa a ƙaramar hukumar da wasu sassan Filato, waɗanda ke yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin al’umma da dama.
BYM ta kuma miƙa gamsuwar ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma jajenta wa al’ummar Dyan, Rim da ma Riyom baki ɗaya.
Kazalika, ta kirayi hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen kama waɗanda suke da hannu aciki al’amarin tare da gurfanar da su don su fuskanci hukuncin doka.
