‘Yan sanda sun kama ‘yar TikTok bisa mutuwar saurayinta a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama tare da fitacciyar mai amfani da TikTok, Fati Cele, bisa zargin ta da hannu a mutuwar saurayinta mai suna Isma’il Makaye a gidan ta da ke unguwar Ɗan Bare a Kano.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce ana cigaba da gudanar da bincike akan al’amarin.

Bayanai sun nuna cewa Fati Cele, ‘yar asalin Jihar Borno ce wadda take zama a wani gida da ta kama haya a unguwar.

Wata majiya ta kusa da mamacin ta bayyana cewa da fari Fati Cele, tayi ihun cewa gobara ta tashi a gidan nata tare da neman ɗaurin jama’a, inda bayan haka ne aka garzaya da saurayin nata zuwa asibitin Nasarawa sakamakon jikkata inda a can aka tabbatar da rasuwar tasa.

Tuni dai aka yi jana’izar Ismail a Unguwa Uku ‘Yan Awaki bayan an miƙa gawarsa ga iyalansa domin yi mata jana’iza kamar yadda addini ya tanada.

By Babaji

Leave a Reply