Wani matashi mai suna Ibrahim Baba, ya kashe maƙwabcinsa, Abubakar Ahmad, bayan ɓarkewar taƙaddama kan jarkar ruwa a unguwar Sabon Titi a Jihar Sakkwato.
Dan uwan mamacin, Umar Ahmad, ya ce marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya da yara biyu, yayin da matarsa ke ɗauke da juna biyu.
Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan marigayin ya ɗauki wata tsohuwar jarkar ruwa da aka ajiye a wajen ɗibar ruwa, ya yanke samanta domin amfani da ita.
Daga baya mai jarkar ta nemi a biya ta kuɗinta tun da an yi amfani da ita.
A cewarsa, marigayin ya amince zai bai wa matar Naira 1,500, amma matar ta ƙi karɓa.
Wani ƙanin mahaifin marigayin ya yi ƙoƙarin biyan kuɗin, amma ta nace cewa sai wanda ya ɗauki jarkar ne zai biya.
Umar, ya ce matar ta kai babban ɗanta, Ibrahim Baba koken abin da ya faru.
“A daren ranar Laraba, marigayin ya fito daga gidansa domin yin fitsari. A lokacin ne Ibrahim da wasu abokansa suka tare shi.
“Sun doka masa sanda a kai, sannan suka sake dukansa har ya mutu,” inji shi.
Ya ƙara da cewa bayan sun tabbatar ya rasu, suka ɗauki gawarsa suka jefa ta cikin harabar wata makarantar Islamiyya da ke kusa da wajen da abun ya faru.
Wani dattijo a yankin, Malam Rufa’i Alhaji Sama’ila Rungumi, ya ce abin takaici ne yadda ƙaramin saɓani ya kai ga kisan kai.
Ya ce wanda aka kashe matashi ne mai sana’ar wankin babura da motoci, kuma yana neman na kansa ne ta hanyar sana’a.
Malam Rufa’i, ya ce bayan gano gawar mamacin a makarantar, an sanar da jami’an tsaro, waɗanda suka kai gawar asibiti. A can aka tabbatar da rasuwarsa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.
