Iyalan Buhari sun koma Kaduna kwanaki 12 da jana’izarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wato A’isha Buhari da tsohuwar matarsa tare da ƴaƴansu, sun yi ƙaura daga Daura zuwa Jihar Kaduna, kwanaki 12 da yin jana’izar tsohon shugaban.

Manyan jami’an gwamnati ne suka marabce su domin girmamawa ga marigayin.

An ruwaito cewa, tsohuwar matar shugaban – Aisha Buhari, ta taho ne tare da ɗanta Yusuf Buhari, ƴarta Zahra Buhari da kuma suaran mambobin iyalan inda suka sauka a sansanin sojojin sama dake Kaduna, ranar Lahadi.

Komawarsu ta nuna kawo ƙarshen jimamin rashin marigayi Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga watanni Yuli a wani asibitin Landon bayan shafe shekaru 82 a duniya.

An yi jana’izarsa ne a gidansa dake mahaifarsa ta Daura a Jihar Katsina a ranar 15 ga watan, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A yayin da suka isa, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, wadda ta jagorancin tawagar jami’an gwamnati ita ta tarbe su a filin saukar jiragen sama na sansanin.

Dakta Hadiza ta jaddada miƙa ta’aziyyar gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ga Aisha da iyalan nata, tana mai alƙawaranta mata samun agajin jihar game al’amuransu.

By Babaji