An buƙaci al’ummar Dawakin Tofa su bada haɗin kai ga riga-kafin zazzaɓin cizon sauro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello Ɗan-Maliki, ya yi kira ga al’umma a ƙaramar hukumar da su bada haɗin-kai wajen gudanar da shirin bayar da maganin riga-kafin zazzaɓin cizon sauro ga yara ƙanana.

Ɗan-Maliki, wanda Shugabar Sashen Kula da Lafiya a Matakin Farko, Hajiya Balaraba B. Gambo, ta wakilta, ya ƙarfafa gwiwar mazauna ƙaramar hukumar da su halarci taron raba gidan sauro da zarar an ƙaddamar da shirin a cibiyoyin da aka ware.

A sanarwar da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Ciyaman ɗin ya kuma buƙaci jami’an lafiya da ke da alhakin raba maganin a gida-gida da su kasance masu adalci da gaskiya wajen hidimta wa al’ummar.

Haka kuma ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa jajircewarta wajen inganta walwalar al’umma a fannoni daban-daban, musamman a kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziƙi.

Kazalika, ya nuna godiyarsa ga Hakimin Dawakin Tofa kuma Madakin Kano, Alhaji Yusuf Ibrahim Ci-gari, bisa ƙoƙarinsa na wayar da kan al’umma kan muhimmancin amfani da gidan sauro yadda ya dace.

Shugabar Sashen Lafiya, Hajiya Balaraba ta jaddada cewa, ya dace iyaye mata su kiyaye katin shaidar karɓar gidan sauro tare da kasa kunne domin sauraron sanarwar da za a yi a nan gaba domin rabon gidan sauro domin inganta lafiyar yara ƙanana da al’umma baki ɗaya.

By Babaji