Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ƙwararrun ’yan fim, mawaƙa da sauran masu sana’o’in ƙirƙira na Arewa da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa goyon bayan nasu zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci gabanta.
Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba, lokacin da ya karɓi tawagar shugabanni da mambobin ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da ke Abuja.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce gwamnatin Tinubu na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen bunƙasa masana’antar ƙirƙira da nishaɗi, ciki har da tallafa wa masu shirya fina-finai, mawaƙa da sauran masu sana’o’in fasaha.
Ya ce Arewa na da damar amfana sosai daga shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar masana’antar ƙirƙira, musamman wajen samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa masu hazaka da kuma kiyaye al’adu.
Shettima ya ce gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa ci gaban masana’antar nishaɗi a yankin Arewa, yana mai jaddada muhimmancin bai wa ’yan fim, mawaƙa da sauran ƙwararrun masana’antar damar bunƙasa sana’o’insu.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce nasarar Tinubu a zaɓen 2027 za ta dogara ne kan ayyuka da nasarorin da gwamnatin ta samu.
Yari ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi la’akari da ayyuka da manufofin gwamnatin kafin yanke matsaya, yana mai cewa yaƙin neman zaɓen wa’adin na biyu na Tinubu zai mayar da hankali kan abin da gwamnatin ta cimma.
Tsohon Gwamnan Katsina kuma Mataimakin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa mai kula da harkokin wayar da kan ’yan Majalisa, Aminu Bello Masari, ya gode wa ’yan masana’antar ƙirƙira bisa goyon bayan da suka bayyana wa Tinubu da sauran ’yan takarar APC.
Masari ya ce manufofin gwamnatin Tinubu na samar da wasu damammaki ga masana’antar ƙirƙira da nishaɗi, inda ya ƙarfafa masu sana’ar da su yi amfani da damammakin da ake samarwa domin bunƙasa rayuwarsu da sana’o’insu.
Tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shi ma ya gode wa tawagar bisa goyon bayanta, tare da kira ga ’yan ƙungiyar da su tsaya kan adalci, daidaito da haɗa kai a yayin gudanar da harkokinsu na siyasa.
Ganduje ya kuma yi kira da a ƙara bunƙasa masana’antar nishaɗi ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da kuma horas da matasa masu tasowa a fannin, musamman a yankin Arewa.
Shugaban ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana aniyar ƙungiyar ta mara wa Tinubu baya wajen neman sake zaɓensa a 2027, tare da tallafa wa sauran ’yan takarar APC a faɗin Arewa.
Rarara ya ce ƙwararrun masu sana’o’in ƙirƙira na Arewa sun haɗa kai wajen gina matsaya guda domin tallafa wa Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar, yana mai cewa goyon bayan da suke bayarwa ya samo asali ne daga yadda suke kallon ayyukan gwamnatin.
Ya ƙara da cewa ƙwararrun masana’antar fim ta Arewa sun haɗa kai wajen tallafa wa ’yan takarar APC a zaɓen 2027.
Shi ma Shugaban ƙasa na ƙungiyar, Alhaji Lawan Ahmad, da Sakataren ƙungiyar, Alhaji Ahmad Bifa, sun bayyana shirinsu na aiki domin samun nasarar Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen da ke tafe.
Sun kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafa wa sake tsara masana’antar ƙirƙira a Arewacin Nijeriya, musamman ta fuskar samar da kayayyakin more rayuwa da inganta jin daɗin masu sana’ar.
