Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya kai ziyara ga Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.
A yayin ziyarar, Mai Martaba Sarkin ya tabbatar wa NAHCON da cikakken goyon bayan masarautar gargajiya, tare da yin kira da a ci gaba da inganta ayyukan Hajji da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da aikin Hajjin maniyyatan Nijeriya.
Sarkin ya yaba wa shugabancin NAHCON bisa ƙoƙarin da yake yi na sake fasalin yadda ake gudanar da ayyukan Hajji, yana mai cewa gudanar da harkokin sufuri da sauran buƙatun dubban mahajjata babban aiki ne da ke buƙatar ƙwarewa, gaskiya da rikon amana, da kuma kyakkyawan tsari.
Ya jaddada cewa Masarautar Zazzau, da kuma hukumomin gargajiya baki ɗaya, na daga cikin manyan masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan maniyyata da kuma shirya su, domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da tsari.
“Hajji tafiya ce mai matuƙar muhimmanci ta ibada, don haka jin daɗi, tsaro da walwalar al’ummarmu yayin gudanar da wannan ibada dole su kasance abin da ya fi komai muhimmanci,” inji Sarkin.
“Mun zo ne domin miƙa addu’o’inmu, shawarwari da goyon bayanmu ga NAHCON. Haka kuma, muna kira ga hukumar da ta ci gaba da ƙoƙarinta wajen inganta tsarin gudanar da ayyukanta, yin shirye-shirye tun da wuri da kuma tabbatar da bayyana sahihan bayanai a fili, domin magance matsalolin gudanar da Hajji da ake yawan fuskanta,” inji shi.
Da yake mayar da martani, Shugaban NAHCON ya nuna matuƙar godiya ga Mai Martaba Sarkin Zazzau bisa wannan ziyara mai muhimmanci, yana mai bayyana ta a matsayin babban ƙarfafa gwiwa ga shugabanci da ma’aikatan hukumar.
Shugaban hukumar ya yi wa Mai Martaba bayani kan sabbin manufofin hukumar, sabbin fasahohin zamani da ake amfani da su, da kuma haɗin gwiwar da hukumar ke yi da wasu abokan hulɗa domin rage kuɗaɗen gudanar da Hajji, inganta masauki da tsarin ciyar da mahajjata, tare da sauƙaƙa jigilar mahajjata ta jiragen sama.
Shugaban NAHCON ya tabbatar wa Mai Martaba Sarkin cewa hukumar za ta duba shawarwari da muhimman bayanan da aka gabatar yayin ganawar, tare da sake jaddada aniyar NAHCON na samar da ingantaccen aikin Hajji na duniya wanda zai dace da tsammanin Gwamnatin Nijeriya da al’ummar Musulmi.
