Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta fayace cewa ba wai an gurfanar da wasu mutane biyar da aka kama a Maiduguri ne kawai saboda sanya rigunan T-shirt masu ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go” ba, sai dai ana tuhumar su da laifukan da suka shafi tayar da tarzoma, karya zaman lafiya, daba da kuma mallakar wasu abubuwa da ake zargin ƙwayoyin miyagun ƙwayoyi ne.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, rundunar ta ce hankalinta ya karkata ga rahotannin da suka yaɗu da kuma muhawarar da lamarin ya haifar a tsakanin jama’a.
A cewar sanarwar, jami’an ’yan sanda da ke sintiri na yau da kullum a cikin garin Maiduguri sun kama mutanen biyar ne a ranar 25 ga Satumba 2026, da misalin ƙarfe 6 na yamma, a yankin West End Roundabout.
Rundunar ta ce an kama mutanen ne bisa zargin aikata wasu abubuwa da ka iya haddasa rikici ko tada hankalin jama’a. A yayin kama su, ’yan sandan sun ce sun samu wasu kayayyaki a hannunsu da suka haɗa da kullin busasshen ganye guda 15 da ake zargin tabar wiwi ne, ƙwayoyi guda 100 da ake zargin D5 ne, tukunyar shisha guda ɗaya, almakashi guda ɗaya da kuma T-shirt guda biyu masu ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”.
Rundunar ta ce bayan kama mutanen, an gudanar da binciken farko inda aka karɓi bayanansu kafin daga bisani a kai ƙarar lamarin gaban kotu.
’Yan sandan sun jaddada cewa rundunar ’yan sandan Nijeriya ƙungiya ce ta ƙwararru kuma ba ta nuna bambanci bisa jam’iyyar siyasa ko ra’ayin siyasa na mutum. Ta kuma ce tana nan daram wajen kare haƙƙin bil’adama, bin doka, tabbatar da tsarin shari’a, riƙon amana da kuma gaskiya wajen gudanar da ayyukanta.
Rundunar ta ce matakin kai lamarin gaban kotu ya kasance ne domin a bar tsarin shari’a ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, tare da yin kira ga jama’a da su dogara da sahihan bayanai, sannan su bar kotu ta yanke hukunci bisa hujjoji da bayanan da za a gabatar mata.
Wannan ƙarin bayani na ’yan sanda ya biyo bayan cece-kuce da suka taso bayan kama mutanen biyar, waɗanda aka bayyana sunayensu da Baba Aji Gremami, Mustapha Abba Yemen, Abbacha Mohammed Ali, Adam Umar Gubio da Abdulhamid Mohammed. Rahotannin farko sun bayyana cewa an kama su ne bisa zargin haɗa kai wajen buga da sanya rigunan da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”.
A cewar rahotannin farko, an tuhumi mutanen da laifukan haɗa baki, tayar da tarzoma, dagula zaman lafiya da kuma daba, bisa wasu sassa na kundin dokokin jihar Borno. An kuma gurfanar da su a gaban kotu tare da tsare su bayan zaman kotun.
Lamarin ya janyo martani daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da kuma wasu ’yan siyasa. ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kama mutanen, tana bayyana tsare su a matsayin matakin da bai dace ba da kuma wanda ke iya tauye ’yancin faɗin ra’ayin siyasa. ƙungiyar ta ce bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana ta hanyar sanya kaya ba laifi ba ne, tare da yin kira da a saki mutanen biyar ba tare da wani sharadi ba.
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shi ma ya yi Allah-wadai da kama mutanen tare da yin kira da a sake su. Atiku ya ce bai kamata a tsare ’yan ƙasa saboda saƙon siyasa da aka rubuta a jikin T-shirt ba, a cewar rahotannin da suka bayyana matsayinsa.
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta dage kan cewa ba wai an gurfanar da mutanen biyar ne kawai saboda mallakar ko sanya rigunan da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go” ba, tana mai cewa ana tuhumar su ne dangane da sauran zarge-zargen da suka haɗa da tayar da tarzoma, karya zaman lafiya, daba da kuma mallakar abubuwan da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
Rundunar ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙwarewa, rashin nuna bambanci, riƙon amana da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yayin da ta bar kotu ta tantance gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa waɗanda ake tuhuma bisa hujjojin da za a gabatar a gabanta.
