
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya shelanta shirinsa na fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda ya ce yana ganin yiwuwar samun nasara matuƙar jam’iyyar ADC ta amince ta ba shi tikitin tsayawa takara.
A wata ganawa ta kafar X da manema labarai, Ameachi ya ce ya san ƙarfi da raunin Tinubu a siyasa saboda ya masa sani na haƙiƙa wanda a cewarsa, zai iya kada shi idan aka yi zaɓe mai cike da gaskiya da adalci.
Haka kuma, Ameachin ya ce bai taɓa sanya hannu a maguɗin zaɓe ba, lamarin da ya sa shi ƙin karɓar tayin shiga sahun kwamitin shirye-shiryen zaɓe na jam’iyyar APC.
“Ina ƙalubalantar duk wani ɗan siyasa, rayyaye ko matacce, da ya zo kusa sannan ya ce ina daga cikin waɗanda suka yi maguɗi.”
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya zargi gwamnoni da hannu a ayyukan da suka shafi maguɗin zaɓe da sauya akalar kuɗaɗen al’umma daga hukumomin gwamnati zuwa na yaƙin neman zaɓe.
Kazalika, ya ci alwashin gudanar da harkar zaɓe mai tsafta da ƙaurace wa dukkan wani abu da ya shafi maguɗi, yana mai ƙalubalantar duk wani ɗan Nijeriya da ya kawo inda aka same shi da hannu a cikin irin haka.
