Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gidauniyar Sauttus Sunnah ta shirya taron na kwanaki biyu da haɗin guiwa da Gwamnatin Jihar Katsina.
A jawabin sa wajen taron Shugaban ƙungiyar JIBWIS ta Jihar katsina Sheik Yakubu Musa Hassan
Ya bayyana cewa
wannan gidauniya ta Sauttus Sunnah ta shirya wannan taro ne mussaman ga matasan mu masu tasowa yadda za’a ɗaura su bisa hanyoyin koyon sana’o’i da kuma gina rayuwar su bisa ga turba ta halal.
Ya sanar da cewa nan gaba wannan gidauniya za ta faɗaɗa irin wannan taron bita zuwa wasu jihohi ƙasar.
Sheikh Yakubu Musa Hassan ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da gudummawa da ta bada wajen wannan taro ya tabbata.
Ya bayyana ayyukan alheri da inganta rayuwar al’umma da gidauniyar ta ke gudanarwa a jihar.
Da yake buɗe taron mai ba wa gwamna shawara a kan harkokin matasa, Hon. Abubakar Tsanni Soja ya nuna jin daɗin shi a kan wannan tunani da gidauniya tayi na shirya wannan taro.
“Hakika irin wannan taron ba ƙaramar gudunmuwa zai bada ba wajen karkato da hankalin matasan mu a kan mahimmanci dogaro da kai ta hanyar koyon sana’o’i kan hanyar da ta dace,”inji Soja.
“Ina mai bada tabbacin gwamnatin Jihar katsina ƙarƙashin ofishina a shirye take wajen bada dukkan gudunmuwar da ta dace wajen inganta rayuwar matasa ta hanyar basu tallafi, koyar dasu sana’o’i da duk gudunmuwar da ta dace,”ya ce.
Mutane da dama ne suka gabatar da jawabai da sa albarka da jan hankali ga matasan wanda suka haɗa da Alh. Mustapha Mai Kudi wakilin kwamandan NDLEA, kwamanda Hisbah Sheik Aminu Usman Abu Ammar, babban sakataren ma’aikatar wassani da matasa Alh. Muhammad Rabi’u Muhammad Sheik Al’Ameen Umar, Malam Abdulrahman Hamza, Hon. Tanimu Sada da dai sauransu.
