Ku faɗa mana yadda ya rasu – Salah ga UEFA kan ta’aziyyar Pelen Falasɗinu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren ɗan wasan nan na ƙungiyar Liverpool, Mohammed Salah ya soki Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Turai (UEFA) bisa ɗora saƙon jimamin rasuwar Suleiman Al-Obeid, da ake kira da ‘Palestinian Pele’, wanda bai ƙunshi cewa harin Isra’ila ne ya rutsa da shi ba.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Falasɗin ta ce, Al-Obeid mai shekaru 41 ya rasu ne bayan wani harin da Isra’ila ta ƙaddamar akan fararen hula da ke jiran samun kayan jin ƙai a kudancin Gaza.

“Adabo ga Suleiman al-Obeid, Pelen Falasɗin”, kamar yadda UEFA ta wallafa a shafin X, ranar Juma’a.

Da ya ke tsokaci akan haka, Salah ya ce “Za ku iya faɗa mana yadda ya rasu, a ina kuma ta yaya?”

Mohammed Salah na ɗaya daga cikin ƴan wasan da ke nuna damuwa game da lamarin yaƙin Gaza, inda shekaru biyu da suka gabata ya bada tallafin wasu maƙudan kuɗaɗe domin agaza wa waɗanda yaƙin ya rutsa da su.

A shekarar 2007 Obeid ya fara buga wa ƙasar Palestine wasa, inda aka fafata da shi a wasanni 24, ya zura kwallo biyu a raga.

Marigayin ɗan wasan ya ci ƙwallaye sama da guda 100 a a yayin da ya ke ƙwallo, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin ƴan ƙwallo daga ƙasar da suka fi haskawa.

By Babaji