NDLEA: An kama fasto da wasu bisa safarar miyagun ƙwayoyi a jihohin Legas, Kano da Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta yi nasara kama Shugaban cocin ‘The Turn of Mercy Church’, wato Adefolusho Aanu Olasele da wasu mutane da dama bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi a jihohin Legas, Kano, Nasarawa da wasu.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi, ya ce an gano cewa faston na da hannu a da dama daga cikin ayyukan safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Nijeriya.

Akan haka ne ya tsere zuwa wata ƙasa don kauce wa kamu, inda daga bisani aka kama shi a ranar 3 ga watan Agusta, 2025 a cocinsa da ke hanyar Okun Ajah zuwa Ogombo a yankin Lekki na Jihar Legas.

Babafemi ya bayyana cewa, tun a watan Yuni ake neman faston ruwa-a-jallo bayan ƙwato wasu miyagun ƙwayoyi da aka alaƙanta su da shi.

A jawabinsa, faston ya amsa cewa yana da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi ta ruwa daga ƙasar Ghana zuwa Nijeriya, sannan sau biyu yana tserewa yayin da aka yi yunƙurin kama shi.

Kakakin NDLEA’n ya cigaba da cewa jami’ansu a yankin Ikoyi, sun yi nasarar kama Benjamin Udo Ukoh da ƙwace ƙwayoyin ‘Canadian Loud’ ɗauri 32 masu nauyin 15.63kg.

Sannan a ranar 9 ga Agusta a Nasarawa, sun kama taba mai nauyin 3,093kg a hannu Emmanuel Asoquo Johnny (51), Okem Raphael (33), da Chekwube Odo (25) a yankin New Karu.

Har’ilayau, a Kano ranar 8 a Agusta, jami’an sun ƙwace taba mai nauyin 359kg a hannun Nura Yahaya (29) a Unguwar Geza, da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso da wasu a sassa daban-daban na ƙasar.

By Babaji