Daga AISHA ASAS
*Na gane wasan kwaikwayon da CP Uche ke yi – Iyabo Ojo
* Zan bayyana batutuwan DNA da Iyabo ta tattauna a sirrance – VDM
*Iyabo Ojo ta rungumi wanda ya kamata ta tambaya – ’Yar uwar Mohbad
*Portable ga VDM: Ka yi watsi da tafarkin adalci ga Mohbad
Sanannen abu ne, mutum kan shahara ne akan abinda yake yi da ya samu karɓuwa ga jama’a, sai su kama sunansa a baki, su sanya soyayyarsa a zuciya, wanda ke kai a wasu lokuta ya rasa walwalarsa sakamakon kowa ya san shi kuma ana muradin ganin shi.
Wannan ne asali kuma sananniyar ma’ana ta shuhura. Kuma tana gushewa ne a dalilin ababe guda biyu, wato mutuwa ko tsawon rai. Sau da yawa za ka samu wani musamman a ɓangaren fina-finai ko waƙa, ya yi fice, ko’ina an san shi, kwatsam sai mutuwa ta sallamo masa. Za a yo jimame da nuna baƙin ciki na ɗan lokaci kafin duk tarin masoyan nasa su rufe babin sa, tamkar ba a yi shi ba.
Haka kuma takan yiwu, yana da rai amma zamani sai ya zo ya wuce shi, sakamakon ya yi tsawon rai, sai shaharar ta gudu ta bar shi.
A ɓangaren mawaƙi Mohbad ko kusa zancen ba haka yake ba, domin duk da kasancewar sa mawaƙi da ya yi waƙoƙin da suka haura biyar, ba kowa ne ya san da zaman sa ba, har sai da mutuwa ta riske shi, inda jama’a da dama suka san cewa akwai wani mawaƙi mai suna Mohbad.
Mutuwar mawaƙin wadda ake zargin kashe shi aka yi ta taɓa mutane da dama, kuma ta harzuƙa su, ciki kuwa da yawa ba su kasance masoyansa ba ko in ce ba su ma san da zamansa ba. Saidai yanayin yadda labarin mutuwar ta zo masu ya sa su tausayi tare da jin ciwon abinda aka ce an masa.
Mutuwar wadda ta tada ƙura mai yawa, har ta yi sanadin zanga-zanga a faɗin Jihar Iko, ta ɗau tsayin lokaci kafin ta lafa, kuma aka bar jin haushin waɗanda ake zargi, wanda za mu iya cewa ya ɗauki tsayin lokacin da har ake tambayar an ya wannan batu zai kai ƙarshe?
A ‘yan watannin baya maganar mutuwar Mohbad ta yanke tamkar an yi ruwa an ɗauke, don haka kowa ya kawar da kansa tunanin kamar kowacce magana da ta shahara a Nijeriya take yin ɓatan dabo ita ma zancen mutuwar ta shiga layi.
Saidai a daidai a ‘yan kwanakin nan an sake dawo da maganar, hakan ya tabbatar da cewa ba tafiya ta yi ba, rashin abin sake faɗa ne ya kwantar da ita, yanzu kuma an samo.
ɗumamen maganar ya soma ne a lokacin da jaruma a masana’antar Nollywood, Iyabo Ojo ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha wurin ganin ta cimma wata madafa dangane da mutuwar mawaƙin.
Fitacciyar jaruma Iyabo Ojo ta bayyana irin gwagwarmayar da ta fuskanta tun bayan mutuwar mawaƙi Mohbad, musamman dangane da faifan muryar da ya bayyana a kafafen sada zumunta. A cewar Iyabo, matar Mohbad, Wunmi, ce ta ɗauki faifan murya da wayar ƙawarta wanda daga baya aka yaɗa shi.
Ta ce, ta bayyana wannan a gaban ’yan sanda kuma ta tabbatar an yi wa Wunmi tambayoyi. Dangane da CCTV a gidan Mohbad, Iyabo ta ce, dangin mawaƙin sun bayyana cewa, ba a saka injin a na’urar ba, kamar yadda itama ta sayi nata gidan ba tare da injin ba.
A lokacin da ta je ofishin ’yan sanda a Abuja, ta ce, an buƙaci da ta yi sulhu da Naira Marley da kuma VDM domin gujewa dogon shari’a. CP Uche, wanda ya taɓa kula da shari’ar ɓatanci da ta shafi Tonto da VDM, ya tambaye ta ko tana da hujjar da ke nuna cewa Naira ne ya kashe Mohbad. Ta ce: “Na faɗa masa ban taɓa cewa Naira ne ya kashe Mohbad ba.”
Duk da wannan buƙatar sulhu da CP Uche ya nema, bai hana ɗaya daga cikin waɗanda ya ambata mayar wa Iyabo da martani ba, wato Very Dark Man.
VDM, wanda ya shahara wajen fafutukar adalci ga marigayi Mohbad, ya mayar da martani ga Iyabo Ojo yana cewa, ficewarta daga tattaunawar WhatsApp ba don faɗan Dre da Samklef ba ne kamar yadda ta faɗa, sai don maganar DNA da ta dabaibaye lamarin.
Ya bayyana cewa, Iyabo ta ci gaba da wallafa abubuwa a cikin group har bayan faɗan Dre da Samklef, ciki har da kalaman ɓatanci da hotunan zargi da ta yi a ranar 13 ga Oktoba. Har ila yau, ya ce, a ranar 11 ga Janairu, Iyabo ta kira mahaifin Mohbad “marar amfani”, sannan ta nuna shiri na fitar da Wunmi daga ƙasar a watan Maris.
Ita ma dai ‘yar uwa a wurin marigayin ta bi layin VDM, inda ta nuna lamarin jaruma Iyabo akwai lauje cikin naɗi, domin aniyarta da aikinta sun bambanta.
Folashade, ’yar uwar marigayi Mohbad, ta caccaki Iyabo Ojo bisa yadda ta sauya akala daga neman adalci zuwa kare matar Mohbad, Wunmi. Ta bayyana cewa Iyabo ta hana Wunmi faɗin gaskiya, kuma ta ɗauke ta zuwa bikin ɗiyarta a daidai lokacin da gawar mijinta ke a ɗakin ajiya.
Ta tambayi Iyabo: “Da ke ce uwarsa, da za ki yi hakan?” Folashade ta koka da yadda Wunmi ta ƙi fitowa ta bayyana abinda ya faru da mijinta bayan mutuwarsa.
Shi kuwa mawaƙi Portable ya zargi VDM da canza sheƙa daga kare marigayi Mohbad.
Portable ya bayyana damuwa kan sauyin matsayi da VDM ya nuna game da marigayi Mohbad. A cewarsa, VDM ya fara ne da fafutukar neman adalci amma yanzu yana zagin marigayin.
Ya ce: “Ka taɓa faɗar inda aka zalunci Mohbad? Ka taɓa fada lokacin da jini ke fita daga jikinsa?” Ya kuma tambaye shi ko yana tsoron Allah, yana mai cewa: “Mutuwa tana zuwa ga kowa.”
