‘Yan sanda sun cafke matashin da ake zargi da kashe ɗalibar Jami’ar Jos

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a garin Jos, babban birnin jihar Filato, sun cafke matashin da ake zargi da kashe wata ɗalibar Jami’ar Jos mai suna Jennifer Anthony.

A ranar Laraba ‘yan sanda suka baje kolin masu laifi da suka haɗa da masu garkuwa da mutane, ‘yan ƙungiyar asiri, masu safarar mutane, ‘yan fashi da makami da kuma Moses Oko ɗan shekara 20 da aka zarga da halaka Jennifer a ranar jajibirin sabuwar shekara.

An ce bayan halaka Jennifer da ya yi, Oko ya kuma ƙwaƙule idanun marigayiyar gami da cire wasu sassan jikinta don cimma buƙatar tsafi.

Bayanan ‘yan sandan sun nuna an cafke matashin ne a Jihar Binuwai inda ya ɓad da kama a matsayin mahaukaci. Bayan da ya shiga hannu ne aka dawo da shi Jos inda ya aikata lafin don ya fuskanci shari’a.

Tuni dai aka yi jana’izar Jennifer a inda take zaman aure a wani yankin jihar Kaduna, amma dai ‘yar asalin jihar Nasarawa ce.