Tsohon gwamnan Oyo, Alao-Akala ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Sahihan rahotanni daga jihar Oyo sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala, ya rasu.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Olatunde Abdulazeez, shi ne ya tabbatar da mutuwar Akala a wata tattauwa da jaridar Punch a ranar Laraba.

Marigayin wanda haifaffen garin Ogbomoso ne kuma ɗan siyasa, ya bar duniya ne yana da shekara 71.

Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa, tsohon gwamnan ya rasu ne a ɗakinsa a Ogbomoso a ranar Laraba bayan fama da ya yi da rashin lafiya.

A halin rayuwarsa, Mr Alao-Akala ya taɓa aikin ɗan sanda, kuma ya yi gwamnan jihar Oyo daga 2007 zuwa 2011.

Kafin zamansa gwamna sai da ya yi mataimakin gwamna ga tsohon gwamna Rashidi Ladoja, tskanin 2003 da 2006, kafin daga bisani aka tsige Mr Ladoja wanda hakan ya bai wa marigayin zama gwamna mai riƙon ƙwarya na tsawon watanni 11.

Kafin mutuwarsa Mr Alao-Akala cikakken ɗan jami’yyar APC ne. Kodayake dai a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu zama gwamnan Oyo, kamar dai yadda ya yi takarar gwamnan jihar ƙarƙarshin jam’iyyar ‘Action Democratic Party’ (ADP) yayin zaɓen 2019.