Hukuma Ƙidaya ta yi takaicin yadda ƙananan hukumomin Abadam da Birnin Gwari suka haddasa tsaikon aiki

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC) ta buƙaci masu ruwa da tsaki, musamman gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya a ɗaukaci faɗin ƙasar nan da su goya wa hukumar baya tare da taimakawa jami’an ta waɗanda a halin yanzu suke gudanar da aiyukan gwajin ƙidaya a zaɓaɓɓun farfajiyar su da aka zaɓa domin gudanar da waɗannan ayyuka.

Shugaban hukumar ta ƙasa, Honorabul Nasir Isa Kwarra ya faɗi a yayin ƙaddamar da qidayar gwajin a hukumance a garin Bauchi shekaranjiya Laraba wajen taron manema labarai a nan Bauchi cewar, ayyukan gwajin ƙidayar wata jarrabawa ce ga hukumar wanda yake fatar za ta haye da gagarumin nasara.

Shugaban, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ƙasa na hukumar mazaunin Bauchi, Ibrahim Mohammed Darazo, ya ji takaicin yadda hukumar ta samu giɓin gudanar da ayyukan ta a cikin ƙananan hukumomi Abadam da Birnin Gwari dake cikin jihohin Borno da Kaduna sakamakon matsalolin rashin tsaro.

Honorabul Nasir Isa ya yi matuƙar fata na samun sauƙin matsalolin tsaro a waɗannan ƙananan hukumomi na Abadam da Birnin Gwari daga yanzu zuwa lokacin gudanar da ƙidayar gamagari ta ƙasa yadda za su shiga cikin wannan gagarumin aiki na ƙidayar jama’ar ƙasa.

Kwarra, ya kuma yi kira ga kafofin watsa labarai dasu haɗa ƙarfi da ƙarfe da hukumar sa domin tabbatar da mafarkin hukumar su na samar da ingantaccen dawwamammun alƙalama waɗanda za su sauƙaƙa, kuma su gurbintar da Nijeriya kan madafun cigaba masu ɗorewa.

Ya shaida wa manema labarai cewar: “Tsammanin mu shine za ku cigaba da yayata shirye-shiryen mu na ƙidayar jama’ar ƙasa mazowa shekarar baɗi bil-haƙƙi da gaskiya kuma cikin gwanicewa domin ku faɗakar da ɗaukacin jama’a ta yadda za a samu gagarumin nasara tare da sauke nauyin wannan muhimmin aiki na ƙasa”.

Kwarra, ya kuma bayyana cewar, ana gudanar da gwajin ƙidayar ne bisa kyakkyawan tsari kusan wa’adin shekara guda gabanin gudanar da ƙidayar na gamagari ta watan Apirilun shekarar baɗi, 2023, domin kimanta fayyace abubuwa da za su kunno kai lokacin gudanar da ainihin ƙidayar.

By Editor