Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Jihar Nasarawa ta bai wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule wata lambar yabo ta musamman wato na tabbatar da zaman lafiya a jihar wadda ta kira ‘Peace Award’ a turance.
Da yake gabatar wa gwamnan lambar yabon a lokicin da ya jagoranci ɗimbin ‘ya’yan ƙungiyar don taya gwamnan murnar bikin sallar bana a gidan gwamnati dake Lafiya, babban birnin jihar, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar a jihar, Alhaji Musa Aliyu wanda aka fi sani da Turaki Gamji ya bayyana wa gwamnan cewa ƙungiyar ta yanke shawarar ziyartar shi ne tare da ba shi lambar yabon don taya shi murnar bikin sallar bana da kuma namijin ƙoƙari da gwamnatinsa ke yi tun da ya hau karagar mulkin jihar wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a duka lungu da saƙon jihar baki ɗaya.
Ya ce ba shakka gwamnan ya cancanci wannan lambar yabo idan aka yi la’akari da ɗimbin nasarori da gwamnatinsa ta kuma cimma a fannonin ayyukan cigaba a duka matakai a faɗin jihar.
Turaki Gamji ya kuma yi amfani da damar inda ya gode wa gwamnan dangane da zaɓinsa da ya yi kwanan nan a matsayin wanda zai ja ragamar shugabancin ‘yan kasuwar na jihar baki ɗaya inda ya tabbatar masa cewa zai yi duka mai yuwa wajen tabbatar da haɗin kan ‘yan kasuwar baki ɗaya don samun nasarori a harkokin kasuwanci a jihar.
Daga nan sai shugaban ‘yan kasuwar, Alhaji Turaki Gamji ya yi alqawari cewa qungiyar za ta cigaba da bai wa gwamnan cikakken goyon baya don tabbatar da nasararsa a zaɓen 2023 dake tafe.
Shi ma da yake jawabi gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule ya yaba wa Turaki Gamji dangane da ɗimbin nasarori da ƙungiyar ta ‘yan kasuwar jihar ta cimma cikin kwanaki ƙalilan da gwamnatinsa ta naɗa shi a matsayin shugaba, inda ya buƙace shi da ya cigaba da haka.
Ya gode wa ‘yan kasuwar a jihar baki ɗaya dangane da ziyarar ta musamman da suka kai masa da kuma lambar yabo na zaman lafiyar da suka bashi, inda ya tabbatar musu cewa hakan ba shakka zai ƙara masa ƙarfin gwiwa ne wajen cigaba da samar wa al’ummar jihar baki ɗaya ribobin dimokaraɗiyya don tabbatar da nasara a duka fannonin rayuwa a jihar.
Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne gwamnan jihar, injiniya Abdullahi Sule ya ƙaddamar da kwamitin riƙo na shugabannin ‘yan kasuwa a jihar da na duka ƙananan hukumomi 13 dake jihar waɗanda suka haɗa da shi shugaban ‘yan kasuwar na jihar, Turaki Gamji da Umar Musa (Awe) da Hassan Sunday (Akwanga) da Asaba Castro (Nasarawa-Eggon) da Ali Ibrahim (Wamba) da Yohana Ishaleku (Obi) da Musa Salihu (Toto) da Bala Aliyu Musa (Keffi) da Ibrahim Yusuf (Karu) da Abubakar Odeh (Doma) da Adamu A. Idi (Keana) Muhammed Balarabe (Nasarawa) da kuma Musa Adamu (Kokona).
