*Litar fetur ta koma Naira 185 a Abuja da Kano
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Masu ababen hawa a Abuja ranar Laraba sun bayyana cewa, an daina samun dogayen layika a gidajen daga jiya Alhamis, inda aka samu ƙarin Naira 20 kan tsohon farashi na Naira 165 a wasu manyan gidajen mai, inda aka wayi gari ya koma Naira 185 maimakon yadda aka saba saye a farashin gwamnati a Kano da Abuja.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, ranar Laraba a Abuja cewa, ga gidajen mai da yawa da suke a kulle babu mai; sai kuma gidajen da akwai mai ɗin irin su AA Rano da A.Y Shafa waɗanda duk suka ƙara fashin fetur ɗin zuwa Naira 185 a kan kowace lita, yayin da shi kuma man dizal suke sayar da kowace lita a kan Naira 850.
Wasu masu ababen hawa sun bayyana cewa gwanda ƙara fashin fetur ɗin akan irin wahalar da suke sha na bin dogon layi, inda ba tare da ɓata lokaci ba mutum zai iya samun fetur ɗin.
Wani matuqin taɗi mai suna Garba Musa ya ce: “Mun riga mun san duk abubuwan da suke shirin yi ke nan, kawai su ƙara fashin mutane ma su huta da wahala. Idan ma ka sayi man wajen ‘yan bumburutu wani lokacin suna gauraya shi da ruwa, wanda sai ya lalata wa mutum injin mota.”
Haka shi ma Amos Enehi ya ce mutane ba su da wani zaɓi a hannun ‘yan kasuwar man fetur. “Muna matuƙar shan wahala a nan Abuja, sai dai ba mu da wani zaɓi, saboda haka za mu sayi fetur ɗin a haka. Muna kira ga gwamnati da ta dubi wannan al’amari don kawo ƙarshen wahalhalun da mutane ke sha, saboda har yanzu mutanen Legas na sayen mai a kan Naira 165 amma me ya sa Abuja ba haka ba?”
Haka ma a Kano, Jaridar Daily Trust ta gano cewa da yawa gidajen man da suka sayar da fetur akan farashin gwamnati na Naira 165 a wancan satin, yanzu sun mayar da shi kan Naira 185, yayin da wasu gidajen suke sayarwa Naira 200, yanzu suna sayarwa Naira 220.
Gidan man Amkar suna sayar da shi akan Naira 220, yayin da gidajen mai irin su AA Rano da Aliko Oil yanzu suna sayar da shi a kan Naira 185 daga Naira 165.
Wani mai sana’ar tuƙi, Malam Salisu Musa ya bayyana cewa ya gano batun ƙarin farashin tun ranar Talata wanda ta shafi rayukan mutane da dama.
Shi ma wani mai abun hawa Usman Abdulkadir Elder, ya ce: “Mun tashi da qarin farashin ranar Talata,” ya bayyana.
Wani mamba a Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN), Oladele Amusan, ya bayyana cewa ‘yan kasuwar ba su da wani zaɓi wanda ya wuce su ƙara fashin don gudanar da gidajen man su, inda ya ce an samu ƙarin fashin ne sakamakon tashin gauron zabin da man dizel ya yi.
A wani labarin mai alaƙa da wannan kuma, Ƙungiyar Manyan Dillalan Mai ta Ƙasa, MOMAN, ta ce ƙayyade farashin litar man fetur kan Naira 165 ba tabbataccen abu ba ne.
Olumide Adeosun, Shugaban MOMAN, ne ya bayyana haka ranar Laraba yayin wani taron ƙara wa juna sani na kariya ga masu siyan mai da Hukumar Kare Cinikayya da Saye ta Tarayya, FCCPC.
Adeosun, wanda ke tsokaci kan matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a faɗin qasar, ya ɗora alhakin lamarin kan rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya kawo cikas ga rarraba makamashi a faɗin duniya.
Shugaban MOMAN ya kwatanta halin da ake ciki a halin yanzu da na lokacin annobar COVID-19, inda wasu ƙasashe suka yi yunƙurin dakatar da fitar da man fetur zuwa ƙasashensu na samar da makamashi na ƙasa.
Ya ci gaba da cewa zai yi wahala a tilasta duk wani nau’in tsarin kula da farashi a kan ‘yan kasuwa, waɗanda sai da su ka yi hovvasar daidaita farashinsu dangane da yadda suke siyan kayayyakin daga rumbunan mai.
Shugaban MOMAN ya ce hanyar da za a bi ita ce gwamnati ta gaggauta ɗaukan matakin janye tallafin mai domin a sauƙaƙa wa masu sayen a ƙasar.
