Kiran Adamu ga Kiristoci: Ku daina fargaba kan tikitin Musulmi da Musulmi

*Sabuwar Gwamnatin APC za ta yi muku adalci, inji Shugaban Jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci mabiya addinin Kirista da su daina wata fargaba a kan tsayar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ta APC, wanda ya kasance Musulmi da Musulmi a matsayin shugaba da mataimaki da jam’iyyar ta tsayar ƙarƙarshin takarar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya na mai ba su tabbacin samun cikakken adalci, idan har APC ta sake kafa gwamnati a 2023.

Shugaban ya ce, yanayin halin da siyasar ƙasar ke ciki ne a yanzu ya janyo hakan, wanda idan har jam’iyyar na son ta ci zaɓen 2023, sai ta yi hakan, amma ba abu ne da wani zai so a ce an yi wannan tsari ba.

Sanata Adamu, ya ce zaɓen Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu, abu ne yin Allah.

A yauin da ya ke yi wa manema labarai bayani bayan wata ganawa ta sirri da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a mahaifar Shugaban Ƙasar ta Daura da ke Jihar Katsina a ranar Laraba, tsohon gwamnan na Nasarawa ya ce, bai kamata wannan zaɓi ya zama abin ƙorafi ba ga al’ummar Kirista.

Ya ce: ”Gaskiyar lamari ita ce, ba abin da Allah yake yi haka kawai. Allah yana da dalilinsa na samar da manyan addinai biyu a ƙasar nan, kuma kowanne daga cikinsu, yana da mutanen da suke da dalilin bin sa kuma suna da haƙƙi su ma.

”Akwai lokacin da Kirista ke jagorantar ƙasar nan. Yanzu kuma lokaci ne da Musulmi ke shugabantar ƙasar. Ba za mu musanta wannan ba. Ba za mu iya samun lallai abin da muke so ba a wani lokaci, a ce dukkaninmu, mun amince da abu ɗaya.’

Ya kuma ƙara da bayanin cewa, ”ba lallai ba ne sai dukkaninmu mun kasance Musulmi ba ko Kiristoci. Nufi ne na Allah a wannan lokacin cewa, Shettima zai kasance mataimakin shugaban wannan babbar ƙasa, idan muka ci zaɓe. Abin da muke fata da kuma addu’a shine cin zaɓe, wanda kuma mu na ƙoƙarin hakan.”

Idan dai za a iya tunawa, a lokacin da ɗan takarar APC, Sanata Tinubu, ya ziyarci Shugaba Buhari a Daura, don yi masa barka da sallah ne ya sanar da Shettima a matsayin mataimakinsa, inda hakan ke nufin dukkan ’yan takarar jam’iyyar Musulmi ne, wato Tinubu da Shettima, lamarin da ya haifar da kace-nace daga wasu mabiya addini Kirista.

A Tarayyar Nijeriya jam’iyyu na da al’adar tsayar da Musulmi daga Arewa, Kirista dage Kudu ne, amma a wannan karon APC ta tsayar da Musulmi daga Kudu ne, lamarin da ta tilasta wa ɗan takarar nata tsayar da wanda suke addini ɗaya daga Arewa.

Tuni dai Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya ta yi allawadai da wannan zaɓi. To, amma Sanata Adamu ya ce, Kiristoci ba za su yi nadama ba a nan gaba, idan har APC ta lashe zaɓen, domin za a yi musu adalci, duk da cewa, shugaba da mataimakin za su kasance Musulmi duka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *