Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alhaji Nasiru Nasko Ɗakingari, tsohon ɗan takarar shugabancin Ƙaramar Hukumar Suru a ƙarƙashin Jam’iyyar APC kuma shugaban matasa daga ƙaramar hukumar, tare da matasa sama da 5,000 da ke goyon bayansa, sun bar Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ta adawa a Jihar Kebbi.
Da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Ɗakingari, Alhaji Nasko ya bayyana cewa, ana zaton adalci a APC, amma sai abin ya zama akasin haka wannan ainihi shi ne babban dalilin da ya sanya suka bar jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa tun da farko sun bayyanawa magoyabayan su da cewa bisa ga alƙawarin da aka yi wa matasa na samun aikin yi da samun abubuwan more rayuwa da cin moriyar dimokuraɗiyya ne ya sanya su goyonbayan Jam’iyyar APC a Kebbi amma sai abin ya zamo kishiyar haka.
“Matasa sun yi cikon fom da Ɗaukar hotunan fasfo ba iyakar tun shekarar 2015 amma a banza kullum ƙaryar yau daban ta gobe daban. Uwa-uba aka zo wajen tsayar da ‘yan takara a 2022 aka yi son rai saboda an hana al’umma su zaɓi waɗanda suke so don su wakilcesu a matakai daban-daban tun kama daga ƙananan hukumomi zuwa jihar da kuma tarayya; haka-zalika a wajen shugabanci.
“A matsayina na shugaban matasa a wannan yankin ba ni da wani zaɓin da ya wuce na bi ra’ayin matasan da na ke ma’amala da su saboda haka sun nemi mu bar jam’iyyar APC zuwa PDP kuma mun fita,” inji shi.
Alhaji Nasiru Nasko Ɗakingari ya bayyana jin daɗinsa bisa ga irin tarba da suka samu a jam’iyyar PDP inda ya ce yanzu haka bayan samun katin shaidar zama ‘yan jam’iyyar kuma tuni waɗansu daga cikin matasan da suka yi hijrar sun sami gurabun takarar muƙamai daban-daban don tinkarar zaɓe mai zuwa.
Wata mai kama da wannan haka-zalika Alhaji Isah Power Kamba ɗaya daga cikin Mambobi kuma Shugaba (Exco) na Jam’iyyar APC da ke Mazaɓar Kamba-Kamba a Ƙaramar Hukumar Mulki ta Dandi ya canja sheƙa daga tsohuwar Jam’iyyarsa ta APC zuwa Jam’iyyar PDP tare da ɗaruruwan magoyabayansa.
Alhaji Isah Power ya bayyana ficewarsa ne a yammacin Lahadin da ta gabata 10 ga wannan watan na Yuli tare da bayyanawa manema labarai irin rashin gaskiya da rashin adalci na tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta ke aiwatarwa faɗin ƙaramar hukumar mulki ta Dandi.
