Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Farashin kayan abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi a Abuja da Jihar Nasarawa, inji rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.
Wani bincike da NAN ta gudanar ya nuna cewa a Nasarawa da Babban Birnin Tarayya, mazauna garin na cikin takaici saboda ƙarin farashin kayan abinci.
Wani ɗan kasuwa a kasuwar Kubwa, Dini Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun wake kan Naira 27,000 amma yanzu a na sayar da shi kan Naira 49,000.
Suleiman ya ce a baya ana sayar da buhun shinkafa ‘yar gida tsakanin Naira 15,000 zuwa Naira 20,000, inda ya ce a yanzu ana sayar da shi kan Naira 29,000, yayin da buhun shinkafar qasar waje da ake sayar da ita kan Naira 25,000 yanzu ta koma Naira 34,000.
Buhun garri mai launin rawaya, wanda aka sayar akan Naira 8,000, a halin yanzu ana sayar da ita kan Naira 22,000 yayin da farin garri da aka sayar akan Naira 6,000 a halin yanzu ana sayar da shi a kan Naira 17,000.
Suleiman ya ce buhun masara a baya ana sayar da shi kan Naira 6,000 yanzu ya koma Naira 20,000.
Ya alaƙanta hauhawar farashin kayan abinci da tsadar sufuri, wanda ya ce hakan ya shafi ƙarfin saye, wanda hakan ya sa farashin kayan abinci ya tashi.
