Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Hukumar Raya Shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ta yi kira ga ɗaukacin matasa marasa ayyukan dake cikin shiyyar da su tsumduma cikin sana’ar bola-jari da zummar rage zaman kashe wando da ya zama katutu a zuƙatan matasan ƙasar nan.
Da yake yin jawabi a bikin rufe bita ta kwanaki bakwai wa ‘yan bola-jari guda ɗari dake Jihar Bauchi kan sabbin matakai cin galaba akan sana’ar ta mayar da bola kuɗi, wani mashawarcin hukumar, Dokta Ahmed Sabo ya buƙaci mahalarta bitar da su yi matuƙar amfani da abubuwan da suka koya domin faɗaɗa kasuwancinsu, har ma da wanzar da tsaftataccen muhalli a cikin al’umma.
Dokta Ahmad Sabo ya bayyana cewar, hukumar ta raya shiyyar za ta samar wa mahalarta bitar kayayyakin sauƙaƙa gudanar da sana’o’insu, ya ƙara da cewar, ana gudanar da makamnancin wannan horaswa a sauran jihohi guda biyar dake cikin shiyyar ta Arewa maso Gabas.
Shi ma da yake yin nasa jawabi, wani wakilin shugaban hukumar a wajen rufe bitar, Mohammed G. Alkali, Dokta Sanusi Ibrahim, ya bayyana cewar, manufar bitar ita ce ta yauƙaƙawa mahalartan fasahohin sana’ar ta mayar da bola kuɗi bisa sauƙaƙan hanyoyi.
Wani malami mai horaswa kan bitar, Dokta Bukar Abba Gana na sashin kimiyyar muhalli na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Bauchi, ya bayyana matufar sarrafa bola domin kiyaye lafiyar jama’a, da kuma kare muhalli daga gurvace wa.
“A yau, ayyukan sarrafa bola sun haɗa da yadda za a samar da alheri daga shara bola, wato, juya bola zuwa dukiya, haɗi da kare muhalli daga gurɓacewar yau da kullum.”
Ya kuma cigaba da cewar: “Ayyukan juya bola zuwa dukiya a garin Bauchi mafi yawan su sun jiɓanci ɗaiɗaikun mutane ne masu zaman kansu da makamantan hukumomi. Duk da haka, ɓangaren gwamnati ma wani jigon mai ruwa da tsaki ne a wannan harka. Gwamnatin jiha a shekara ta 2012 ta kafa wani katafaren kamfani kan kuɗi miliyan N244 wanda yake sabunta tarkacen robobin bola zuwa sabbin kayayyakin aikatau”.
Wasu daga cikin mahalarta bitar, Anas Mohammed Bakaro, Amina Saleh da Amadu Mohammed Doya sun yabawa hukumar ta raya shiyyar arewa-maso-gabas, tare da bata tabbacin yin amfani da ilimin da suka koya, yayin da wani mahalarcin, Ahmad Chinade yake cewa, horaswar ta yi masa matuqar tagomashi, da alƙawarin cewa shi ma zai yaɗa ilimin wa waɗansu a unguwarsu.
Darakta-Janar dake Shugabancin Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA), Dokta Kabiru Ibrahim Gamawa ya yi matuƙar yabawa hukumar ta NEDC bisa yin tarayya da gwamnatin jiha a manyan fannonin cigaba daban-daban.
Sakataren Dindindin a Ma’aikatar Gidaje da Muhalli ta jihar Bauchi, Suleiman M. Babaji Esq ya lura da cewar, shirya irin wannan bita da hukumar raya shiyya tayi, wata manuniya ce ta sadaukar warta ga manufofin gwamnatin jihar Bauchi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.
Babaji ya kuma lura da cewar, yana cikin qudurin hukumar ta NEDC na samar da ɗorarren muhalli ba ga wannan al’umma kaɗai ba, har ma da al’ummar da za ta taho nan gaba, wanda shine maƙasudin wannan horaswa ta matasa.
Mahalartan wannan bita ta Bauchi dai, an zaƙulo su ne daga ɗaukacin ƙananan hukumomi ashirin dake cikin jihar, kuma kowannen su za a ba shi takarda ta shaidar kammala bitar da take da tarin albarka.
