Dalilin da ya sa muka kai hari kurkukun Kuje – ’Yan bindiga

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindigar da suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja ranar Talata, sun bayyana cewa sun kai hari ne don su kuɓutar da mutanensu saboda sun ga shugaban ƙasa yana yi wa gaggan ɓarayi afuwa. 

Wata majiya mai tushe ta ruwaito wasu masu tsaron gidan yarin na Kuje suna bayyana cewa sun ji ‘yan bindigar suna fadar haka a lokacin da suka kai harin. 

Manhaja ta bada rahoton cewa ‘yan bindigar sun fitar da mutane kusan 900, yayin da sama 300 suka dawo. Daga ciki, 69 kwamandojin Boko Haram ne. 

A lokacin harin na tsawon biyu,’ ‘yan bindigar sun kwashe tsawon mintuna 20 suna yi wa tsararrun wa’azi, tare da bin daki-daki suna fito da mutanensu. 

Majiyar tamu ta ce ‘yan ta’addan sun fada masu cewa tun da Shugaban Ƙasa Buhari ya iya yafe wa manyan ɓarayin ƙasa, ba su ga dalilin da zai ya riƙe masu shugabanninsu ba.

Suka ce gwamnati ba Allah ba ce, domin shi ne kaɗai ke hukunta bayinsa.

A watan Afrilu ne Shugaba Buhari ya yafe wa wasu gaggan varayi, ciki har da tsaffin gwamnoni, Jolly Nyame da Joshua Dariye aka samu da laifin sace kuɗaɗen jihohinsu. 

Tuni dai gwamnatin ta fitar da jerin sunayen da hotunan ‘yan Boko Haram 69 da maharan suka kuvutar a harin na makon jiya. 

By Editor