Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, ya buƙaci ‘yan Nijeriya su duƙufa wajen gudanar da addu’o’i ga Allah Mabuwayi gagara misali ya kawo ƙarshen matsalolin ta’addanci da suke cusa tsoro da fargaba a zukatun jama’ar ƙasar.
Sarkin na Bauchi ya yi kuma kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da cewa, ba tare da la’akari da nasabar addini ko ƙabilanci ba, su cuɗanya da juna cikin zamantakewa, haɗi da guje wa shiga sharo ba shanu da zai haddasa zaman ɗar-ɗar da ban tsoro da za su daƙushe walwalar jama’a.
Mai Martaba Rilwanu Adamu, wanda kuma shine shugaban jiha na reshen Jama’atu Nasril Islam (JNI) ya yi waɗannan koke ne a cikin wata takardar jawabi da sakataren ƙungiyar ta jiha, Injiniya Ahmad Jumba ya rattava hannu, ya ƙara da yin kira ga jama’ar Jihar Bauchi da su yi koyi da koyarwar Annabi Ibrahim da sadaukarwa irin ta ɗansa Annabi Isma’il domin tallafawa junan su a dukkan lokutan rayuwa.
Jawabin na Sarkin Bauchi ya yi kuma kira ga shugabannin addini da na siyasa su yi kaffa-kaffa da ire-iren abubuwan da ke fitowa daga bakunansu da zummar wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma, wanda shine jigon cigaban jama’a.
Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya kuma jaddada buƙatar ‘yan siyasa su riƙa bin ƙa’idojin harkokin siyasa, musamman lokacin yaƙin neman zaɓe, ta yadda masu jefa ƙuri’a za su fahimci saqonni da manufofinsu.
A wani cigaban kuma, Gwamna Bala Mohammed ya buƙaci jama’a da su ɗauki halayin yin afuwa, tawali’u da mutunta juna, haɗi da addu’o’i domin ɗorewar zaman lafiya, da addu’o’in samun damina mai albarka.
Gwamna Bala, a cikin saƙonsa na Sallah Layya, ya yi tuni da cewar, Alƙur’ani mai girma ya umarci dukkan Musulmi da su riƙa bayar da sadaka daga cikin dukiya da Allah ya huwace masu, ba tare da yin la’akari da bambancin addini, ƙabila ko siyasa ba.
Mohammed ya bayyana cewar, sallar layya bikine na ɗaya a shekara da ake yi domin tunawa da sadaukarwa na Annabi Ibrahim (AS) wa Mahaliccin sa lokacin da aka umarce shi da ya yanka ɗansa Annabi Isma’il, yana mai bayyana cewar, wannan shine mafi girman sadaukantar wa ga umarnin Ubangiji.
Ya ce wannan sadaukarwa abin koyi ce, musamman ga Musulmi, yana mai cewar, ana yin dubi da sallar layya ne domin lura da yadda muka wanzar da halayenmu cikin wa’adin shekara guda da ta shuɗe domin gyara kura-kuren da muka tabka a cikinta, da zummar yin gyara a cikin shekara da za mu shiga domin samun falalar Ubangijin talikai.
Gwamna Bala, yayin da yake yin kira ga ɗaukacin Musulmi da su qarfafa dangantaka dake wanzuwa a tsakaninsu, da kuma bijiro da sabbin hanyoyi na ƙarfafa zumunci, ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da yi wa jama’a hidimomi, da kuma nusar da cigaban jihar Bauchi zuwa matakan yabawa.
“Za ku iya yarda da ni cewar, tun zuwanmu bisa karagar mulki yau kusan shekaru uku da suka gabata muke ta inganta cigaban jiha da samar da romon dimokraɗiyya a fannonin rayuwa daban-daban da suka haɗa da bayar da ilimi, inganta kiwon lafiya, samar da tsaftataccen ruwan sha, ƙarfafa mata da matasa, samar da gidaje da duƙufa ga ayyukan noma, dadai sauransu”.
Waɗannan nasarori, inji gwamnan, sun kasance jigo kuma shamaki wa cigaban jihar Bauchi, yana mai bayar da tabbacin cigaba da aiwatar da ayyuka masu sanya ɗamba wa ɗaukacin rayuwar jama’ar jihar Bauchi a cikin ragowar wa’adin farko na wannan gwamnati.
Mohammed sai ya ce: “Haƙiƙa muna sane da matsin tattalin arziki dake gundarar jama’a. Wannan lamari ne tamkar ruwan dare gama duniya da yake da asali daga cutar sarƙewar numfashi da ya riƙa rikita lissafin jama’a tun daga shekara ta 2020. Ina mai son jan hankalin ku da a cigaba da yin haƙuri domin wannan annoba ce ta wicin-gadi, mai wucewa”.
Gwamna Bala ya bayyana cewar, a matsayin ta na gwamnati dake sane da haƙƙin jama’a, za a cigaba da ɗaukar matakan samar da tallafi wa jama’a domin rage nauyin raɗaɗi dake addabarsu, sai ya roƙi jama’a da su kasance masu sadaukantar wa domin shawo kan lamura da suka yi tsanani.
