Za a shirya babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya a Ƙasar Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

A shekarar 2002 ne hukumar kula da abinci da aikin gona ta MƊD(FOA) ta gabatar da wata shawara dangane da muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya. A bana ne, aka cika shekaru 20 da gabatar da wannan shawara.

Daga ranar 17 zuwa 19 ga wata, za a gudanar da babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na ƙasa da ƙasa a gundumar Qingtian ta lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, babban taken taron shi ne, kiyaye al’adun gargajiya na aikin gona tare da kara azama kan farfadowar yankunan karkara daga dukkan fannoni.

Muhimman al’adun gargajiya da suka shafi aikin gona na ƙasa da ƙasa, wasu tsare-tsaren gargajiya ne na aikin gona, waɗanda suke da daraja sosai a fannin al’adu da tarihi, waɗanda kuma suka kasance a matsayin abubuwan koyi a fannin aikin gona na zamani, inda aka haɗa aikin shuke-shuke, aikin kiwon dabbobi, kiwon kifi da aikin sarrafawa waje guda.

Ya zuwa yanzu, akwai muhimman al’adun gargajiya 18 da suka shafi aikin gona a ƙasar Sin, adadin dake kan gaba a duniya.

Shugaban sashen haɗin gwiwa da ƙasashen duniya na ma’aikatar noma da yankunan karkara ta ƙasar Sin, Sui Pengfei ya bayyana fatan ganin an yi amfani da babban taron, a matsayin dandalin musayar ra’ayoyi da hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban,da cimma matsayi guda tsakanin ƙasa da ƙasa kan daukar matakin bai daya, da faɗaɗa ayyukan farfado da yankunan karkara, da yayata da gadon al’adun aikin gona, da yin koyi da juna.

Sui ya ce, “A yayin babban taron, za a yi musayar ra’ayoyi kan matakan da kasashen duniya suke dauka a fannonin yin amfani da al’adun gargajiya na aikin gona, wajen kyautata tsarin samar da abinci, da kara samar da ci gaba mai dorewa a yankunan karkara, da kyautata zaman rayuwar manoma, a kokarin ganin an wadatar da yankunan karkara tare. Muna fatan za a yi amfani da babban taron, wajen kara tuntubar juna don fito da sabbin dabaru a fannoni masu ruwa da tsaki.”

Fassarawar Tasallah Yuan

By Editor