Daga CMG HAUSA
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce batun da ake kira da wai tarkon bashi na ƙasar Sin, batu ne kawai da masu adawa da dangantakar Sin da ƙasashe masu tasowa a Afrika da wasu yankuna don gaggauta samun ci gaba, suka ƙirƙiro.
Wang Wenbin, ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Laraba.
Rahotanni na cewa, wani rahoto da Gidauniyar Debt Justice ta Birtaniya, mai bibiyar harkokin da suka shafi bayar da bashi ba bisa adalci ba, ta fitar, ya zayyano wasu bayanai daga Bankin Duniya da asusun IMF da wasu cibiyoyi, inda suka nuna cewa, bashin da ƙasashen Afrika suka karba daga cibiyoyin kuɗi masu zaman kansu a ƙasashen yamma, sun ninka yawan bashin da suka karɓa daga ƙasar Sin hau sau 3, haka kuma kuɗin ruwansu ya ninka na Sin sau biyu.
Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
