Daga LUBABATU LEI
Hukumar kula da shirin abinci ta MƊD (WFP) ta yi gargaɗi a kwanan baya cewa, ‘yan Adam ka iya fuskantar “matsalar abinci mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu”. Matsalar kuma ta fi yin tasiri ga ƙasashen Afirka.
Hauhawar farashin abinci a sakamakon matsalar ƙarancin abinci na matuƙar addabar al’umma, musamman na ƙasashen da ke fama da rashin ci gaba.
Amma kuma manyan kamfanonin hada hadar cinikin abinci na duniya na cin muguwar riba sabo da matsalar. Daga cikin manyan kamfanonin cinikin abinci mafiya girma guda huɗu na duniya, wadanda ke shafar kimanin kaso 75% zuwa 90% na cinikin abinci na duniya, akwai guda uku da suka kasance na ƙasar Amurka, waɗanda suka haɗa da ADM da Bunge da Cargill.
Sai dai sakamakon matsalar ƙarancin abinci da hauhawar farashinsa, akwai mutane uku ‘yan gidan masu kamfanin Cargill da kadarorinsu suka ƙaru da kimanin kaso 20% a wannan shekara, lamarin da ya sa suka shiga jerin mutane 500 mafi arziki a duniya. Baya ga haka, sauran kamfanonin biyu sun samu matuƙar hauhawar farashin hannayen jarinsu.
Tsohon sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka, Henry Alfred Kissinger ya taba cewa, “Wanda ya mallaki man fetur, ya mallaki ƙasashen duniya, kuma wanda ya samu iko a kan takardun kuɗi, ya samu iko a kan tattalin arzikin duniya, yayin da kuma wanda ya mallaki abinci, ya samu iko a kan ‘yan Adam.”
A haƙiƙa, ana iya gano hannun Amurka a matsalolin ƙarancin abinci da aka fuskanta a tarihi.
Ta hanyar ingiza abin da ake kira wai “ciniki mai ‘yanci”, da kuma fitar da irin da aka ƙirƙiro waɗanda ba su iya haiyayyafa ba da kuma fasahohin noma na musamman, Amurka ta lalata tushen aikin noma na ƙasashe a tasowa, waɗanda har suka ƙasa dogara da kansu, tare da ƙara dogara da ita wajen samar da abinci. Ta hakan kuwa, Amurka ta samu iko a kan farashin abinci na duniya har da tsarin samar da abincin, kuma ta yi babakere a wannan fanni.
Mai zane: Mustapha Bulama
