Yadda taron bada kyaututtuka ga zakarun gasar rubutacciyar waƙa ya gudana

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Ƙungiyar Gamayyar Marubuta da Manazarta waƙoƙin Hausa reshen Jihar Kano, ta gudanar da taron bada kyaututtuka ga zakarun gasar rubutacciyar waqa da suka sanya akan Illolin fyaɗe da cin zarafin mata.

Taron wanda ya gudana a American Space da ke ɗakin karatu na Murtala Muhammad Laburare, Kano a ranar Lahadin da ta gabata.

Gasar mai jigo akan ‘Illolin fyaɗe da yadda za a magance su’. An samu ‘yan takara guda 15, maza 10, mata 5.

Muhammad Lawan PRP shine ya zama zakara da waƙarsa mai suna ‘Bulaliya” da maki 235. Sai Nasir Usman Babaye da ya zo a matsayi na 2 da waƙarsa mai suna ‘Kukan zuciya’ da maki 233. Rahama Ahmad Muhammad ita ce ta zo a matsayi ta 3 da waƙarta mai suna ‘Mazariya’ da maki 231.

Farfesa Ibrahim G. Satatima wanda shi ne baƙo mai jawabi ya ce, bahaushe bai samu rubutacciyar waƙa ba sai bayan ya iya karatu da rubutu ne ya ba shi dama yake iya ɗaukar alƙalami ya yi amfani da takarda ya rubuta waƙa, don haka ya ce, Bahaushe da ya damfara da rubutu da karatu ya fara buɗar ido ne da rubutun Larabci, wanda su kuma suna da turakun ma’aunai guda 10, sannan da koguna guda 16.

Ya ƙara da cewa, “daga cikin muhimman batutuwa da suke taimakawa a fahimci waƙa shine, marubucin ya zama yana da ilimin rubutu da karatu, domin ta haka ne saƙon da ke cikin waƙar zai isa ga al’umma.”

Tun da farko a jawabinsa, shugaban ƙungiyar na Jihar Kano, Ibrahim Hamisu ya ce, sun shirya gasar ne domin ƙarfafa gwiwa da kuma zaƙulo sabbin marubuta waƙoƙin Hausa a cikin al’umma.”

Taron dai ya samu halarta malaman jami’a da kwaleji kwaleji da kuma manyan marubuta da ke faɗin Jihar Kano da kuma maƙwabta.

By Editor