An shirya taron farko na ƙaramin kwamitin aikin gona na kwamitin gwamnatocin ƙasashen Sin da Nijeriya

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, aka gudanar da taro na farko na karamin kwamitin aikin gona, na kwamitin gwamnatocin ƙasashen Sin da Najeriya ta kafar bidiyo.

A yayin taron, ɓangarorin biyu sun waiwayi nasarorin da aka cimma, a hadin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a fannonin amfani da fasahohin aikin gona, da cinikayyar noma, da ingancin abinci, da horar da ƙwararru, da kuma manyan ababen more rayuwa da dai sauransu, tare da yin mu’amala sosai kan ƙara sa ƙaimi, ga ciyar da hadin kai mai inganci a ƙasashen Sin da Najeriya gaba.

Kana ɓangarorin biyu sun bayyana aniyarsu, ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa, da zurfafa alaƙa, da ayyukan da suka shafi “Ayyuka tara”, na taron ministoci karo na takwas, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, waɗanda aikin haɗin kan laimar kwaɗo ya wakilta, ta yadda za a ci gaba da kyautata jin daɗin jama’ar ƙasashen biyu, da sa kaimi ga bunƙasuwar dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu yadda ya kamata.

Mataimakin ministan noma da yankunan karkara na ƙasar Sin Ma Youxiang, da babban sakatare a ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta ƙasar Najeriya Ernest Afolabi Umakhihe ne suka jagoranci taron. Shi ma Ambasada Cui Jianchun daga ofishin jakadancin ƙasar Sin dake Najeriya ya halarci taron ta yanar gizo.

Mai fassara: Bilkisu Xin

By Editor