Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ce ƙasar sa a shirye take ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Rasha a fannin makamashi.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, cikin sakon da ya aike ga taron dandalin cinikayyar makamashi na Sin da Rasha karo na 4, ya ce haɗin gwiwa a fannin makamashi muhimmin jigo ne na haɗin gwiwar sassan 2, kuma muhimmin ƙarfi dake iya tabbatar da isasshen makamashi a duniya.
Cikin wasiƙar tasa, shugaban na Sin ya ƙara da cewa, yayin da ake fuskantar haɗurra da ƙalubale daga sassan waje, Sin da Rasha sun ƙarfafa tuntubar juna, tare da ingiza ayyukan haɗin gwiwa, wanda hakan ke nuni ga juriyar da haɗin gwiwar su ke da ita a fannin makamashi, da ma sauran manyan abubuwan da suka sanya gaba cikin haɗin gwiwarsu, bisa manyan tsare-tsare a sabon karni.
Mai fassara: Saminu Alhassan
