Ya kamata Birtaniya ta waiwayi tarihi domin ɗaukar darasi

Spread the love

Daga FA’IZA MUSTAPHA

A cikin wannan mako ne ake sa ran shugaban Tarayyar Turai, Charles Micheal, zai ziyarci ƙasar Sin, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa.

Wannan wani babban ci gaba ne a dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, inda a karon farko, yawan cinikayya a tsakaninsu cikin shekarar da ta gabata, ya zarce dala biliyan 800, kana jari tsakanin ɓangarorin biyu, ya zarce dala biliyan 270.

Lallai wannan ya shaida yadda cinikayya da kyakkyawar dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu ke kyautata da kara farfaɗowa tare da haifar da ɗimbin sakamako da ribar moriyar juna.

Sai dai a daidai wannan lokaci ne kuma, aka jiyo sabon Firaministan Birtaniya Rishi Sunak, ya na wasu furuci da suka sauka daga kan turba, inda yake bayyana ƙasar Sin a matsayin barazana ga martaba da kimar ƙasashen yamma.

Idan har iƙirarin da yake yi gaskiya ne, ta yaya aka samu ƙaruwar waɗancan alkaluma na cinikayya tsakanin ɓangarorin biyu?

Tun da ya hau karagar mulki, ya ke bayyana ƙasar Sin a matsayin ƙalubale.

Shin manufofin kasashen waje al’ummar Birtaniya suka damu da shi, ko kuma kyautatuwar zaman takewarsu?

Firaministan na kaucewa ainihin alhakin da ya rataya a wuyansa na kula da al’umma da jagorantar ƙasarsa wajen samun ci gaba, inda yake mayar da hankali kan ƙasar Sin, wadda ba komai take nema ba, face zaman lafiya da haɗin gwiwa da ci gaba na bai ɗaya.

Ya ƙara da cewa, cinikayya tsakanin ɓangarorin biyu zai fuskanci sauye-sauye.

An dai ga yadda Amurka ta tayar da rikicin cinikayya tsakaninta da Sin, kuma an ga gurguwar sakamakon da hakan ya haifar, inda ‘yan kasuwar ƙasar suka ji raɗaɗin a jikinsu.

Duniya na fuskantar tarin ƙalubale da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki da masassarar tattalin arziki da yunwa da matsalar sauyin yanayi da makamashi, waɗanda ba su bar kowacce ƙasa a baya ba.

A wannan lokaci, kamata ya yi a haɗa hannu da ajiye bambance-bambance, wajen lalubo mafita tun kafin a rasa tudun dafawa.

Duk da waɗannan ƙalubale dai, ƙasar Sin ta na kara ɗaukar manufofin raya kanta da kyautata rayuwar al’ummarta, kuma cikin manufofin nata, har da ƙara faɗaɗa bude kofarta ga kasashen waje.

Rufe ƙofa dai ko ɗaukar ra’ayi na kashin kai ko kariyar cinikayya, sun riga sun shaida mana cewa, babu abun da suke haifarwa face koma baya.

Kamata ya yi firaministan na Birtaniya, ya sake nazari ya waiwayi tarihi, ya kuma zame masa darasi.

By Editor