Sin ta nuna kyakkyawar alƙiblar yaƙi da mummunan tasirin sauyin yanayi

Daga SAMINU HASSAN

A ’yan shekarun baya-bayan nan, hankulan duniya na kara karkata ga zaƙulo dabarun dakile ƙalubalen sauyin yanayi, ƙarƙashin haɗin gwiwar dukkanin sassan ƙasa da ƙasa.

Kuma a bana, yunkurin ƙasashen duniya a wannan fanni ya ƙarfafa, sakamakon taron COP27 na ɓangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD da aka gudanar a baya bayan nan a ƙasar Masar, wanda ya kasance babban dandali ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki, na hada ƙarfi da ƙarfe wajen lalubo dabarun gaggawa na shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi.

Ma’anar sauyin yanayi
Sauyin yanayi na nufin sauyi mai tsawo na zafi, da sauran abubuwa masu alaka da jirkitawar yanayin muhalli na ainihi.

Wannan sauyi na iya zama mataki da zai auku ba tare da sa hannun bil adama ba.

Sai dai tun daga shekarun 1800, ayyukan yau da kullum na dan adam sun zamo a sahun gaba wajen ingiza sauyin yanayi, musamman ta hanyar ƙona albarkatun mai da kwal, waɗanda dukkanin suke fitar da nau’o’in iska mai ɗumama yanayi da sauya yanayin duniya na asali.

Masana na cewa, ɓangaren ƙona albarkatun mai shi ne kan gaba da kaso mafi rinyaje cikin abubuwan dake haifar da sauyin yanayi, domin kuwa ta ƙarƙashin wannan fanni ake fitar da kaso sama da 75 bisa ɗari na nau’o’in iska mai dumama yanayi, da ma kusan kaso 90 bisa dari na iskar “carbon dioxide”.

Masana na cewa nau’o’in iska masu ɗumama yanayi na lalluɓe duniyar bil adama, tare da kange zafin rana daga ficewa daga doron duniya.

Dalilan dake haifar da sauyin yanayi
Masana da masu bincike sun tabbatar da cewa, muhimman dalilan dake haifar da sauyin yanayi sun haɗa da ayyukan sarrafa makamashi domin samar da lantarki, da kona albarkatun mai a masanaantu, da gidaje da ababen hawa.

Har ila yau, akwai batun sare dazuzzuka, inda alƙaluma suka nuna cewa, a duk shekara bisa kiyasi, ana sare faɗin daji da ya kai hekta miliyan 12. Kuma da yake dazuzzuka na zuke iskar carbon dioxide mai ɗumama yanayi, sare dazuzzukan na mayar da hannun agogo baya, a yunkurin da ake yi na magance wannan ƙalubale.

Masana sun ce sare dazuzzuka, tare da ayyukan noma, da sauran ayyukan da bil adama ke yi domin amfanin yau da kullum, su ne ke haifar da kaso ɗaya bisa huɗu na nauo’in iska mai ɗumama yanayi dake addabar duniya.

A ɗaya ɓangaren kuwa, masana na cewa, ko shakka babu idan har bil adama na son ganin bayan tasirin sauyin yanayi, wajibi ne ya mayar da hankali ga daƙile dumamar yanayi ta hanyar bunƙasa samar da makamashi daga ƙarfin iska, da hasken rana, da sauran nau’o’in makamashi da ake iya sabunta amfani da su.

An dai yi ittifaƙi cewa, ya zama dole dukkanin sassan duniya su yi haɗin gwiwa da juna, wajen gano dabarun rage raɗaɗin sauyin yanayin, da gano fasahohin kimiyya, da na zamantakewa, waɗanda za su baiwa dan adam damar jurewa, da ɗorewar rayuwa tare da ƙalubale masu nasaba da sauyin yanayi, da lalubo dabarun rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa ga alummun duniya a nan gaba, da ma batun samar da kuɗaɗen gudanar da wadannan ayyuka.

Kazalika an yi amannar cewa, nahiyar Afirka da sauran sassan ƙasashe masu tasowa, na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi ƙarancin sinadarai, da nauo’in iska mai gurbata, ko dumama yanayin muhallin duniya, amma a hannu guda, nahiyar da ma wasu ƙasashe marasa sukuni, su ne a sahun gaba wajen ɗanɗana kuɗa daga mummunan tasirin sauyin yanayi.

Alƙaluma sun nuna cewa, ƙasashen masu ci gaban masana’antu da suka haɗa da Sin, da Amurka, da Indiya, da Rasha, da Japan, da Jamus, da Iran, su ne kan gaba wajen fitar da sinadarai, da nauo’in iska mai gurbata, ko ɗumama yanayin muhallin duniya.

A bana, sassan Turai sun fuskanci ƙaruwar zafi mafi muni a tarihi, da gobarar daji, kana ƙasashen Najeriya da Nijar da Pakistan sun fuskanci ambaliyar ruwa da aka jima ba a ga irinta ba, wasu sassan duniya kuwa sun fuskanci ƙaruwar mahaukaciyar guguwa mai haɗe da tumbatsar teku da ambaliya.

Buga da kari, ƙasashen Kenya da Habasha a gabashin Afirka, na ci gaba da fuskantar fari mafi muni cikin shekaru masu yawa.

A cewar shirin abinci da aikin gona na MƊD ko WFP, adadin mutane daga yankin kahon Afirka dake fama da ƙarancin abinci, ya ƙaru daga mutum miliyan 135 a shekarar 2019 zuwa mutum miliyan 345 a yanzu.

Wannan wani ɓangare ne kawai, na jimillar alummun duniya da yawansu ya kai miliyan 50 daga ƙasashe 45 dake fuskantar barazanar faɗawa yanayi na fari.

An samu aukuwar gobarar daji a sassan da dama na Turai da Amurka
A bana ambaliyar ruwa ta shafi sama da jihohin Najeriya 20
Fari mai tsanani ya raba dubun dabatar al’ummun gabashin Afirka daga muhallan su

A jimlace, sauyin yanayi na haifar da ƙamfar ruwa a sassan duniya daban daban, yana haifar da ƙaruwar zafi, da fari wanda ke shafar yawan yabanyar da ake iya samu daga ayyukan noma, da lalacewar muhallin halittu, da kwararar hamada.

Kaza lika sauyin yanayi na haifar da ƙaruwar barazanar ambaliyar teku, da bacewar wasu nau’o’in tsirrai da halittu, da ƙamfar cimaka tsakanin al’ummun duniya.

Bugu da kari, sauyin yanayi na haifar da barazanar ɓarkewar cututtuka masu nasaba da gurbacewar iskar shaka.

A duk shekara, yanayin sauyawar muhalli na sabbaba rasuwar mutane kusan miliyan 13 a sassa daban daban na duniya.

Haka kuma, sauyawar salon yanayin muhalli yana ingiza bazuwar cututtuka, irin waɗanda ke fin ƙarfin tsarin kiwon lafiya da bil Adama ke da shi.

A ɗaya hannu kuma, mutane da dama na ƙaurace wa muhallansu sakamakon matsalolin dake tattare da tasirin sauyin yanayi, ta yadda hakan ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa, da gurguncewar tattalin arzikinsu.

Da yake ƙasashe masu sukuni ne kan gaba wajen gudanar da ayyuka dake haifar da gurbatar yanayi, an yi ta gudanar da taruka na ƙasa da ƙasa da nufin tattaunawa wannan matsala, tare da yin kiraye-kiraye na samar da kuɗaɗen diyya ga ƙasashe masu tasowa da matalauta, ta yadda za su samu damar rage raɗaɗi wannan matsala.

Bayan tattaunawa da gudanar da shawarwari masu yawa, ƙasashen duniya sun ƙaddamar da taron shekara-shekara game da sauyin yanayi, ƙarƙashin yarjejeniyar yanayi ta MƊD, wadda aka amince da ita a shekarar 1992.

Ƙarƙashin wannan yarjejeniya ne kuma gwamnatocin ƙasashe daban daban, suka amince da aiwatar da manufofi na takaita ƙaruwar ma’au’in zafi, da matakan daƙile munanan tasirin sauyin yanayi.

Kazalika ƙarƙashin dandalin ƙasashen da suka amince da wannan yarjejeniya, an kafa asusun musamman na tallafawa sassan da suke tafka asara sakamakon tasirin sauyin yanayi.

Duk da cewa asusun bai yi tasirin da ya kamata ba, sakamakon gaza cika alƙawuran samar da kuɗaɗen aiwatar da shi, a hannu guda, ya zamo tamkar sanya ɗan-ba ga ayyukan da suka biyo baya a fannin.

Tsakanin ranakun 6 zuwa 20 ga watan Nuwamban bana, an kira taro na 27, na ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD ko UNFCCC a birnin Sharm El Sheikh na ƙasar Masar.

Kuma gabanin kammalarsa, ƙasashe mahalarta sun amince da kafa sabon asusun musamman, wanda zai tattara kuɗaɗen tallafawa ƙasashen dake fuskantar barazanar sauyin yanayi, ta yadda za su iya tunkarar ayyukan yaki da tasirinsa yadda ya kamata.

An cimma matsayar cewa, asusun zai samar da kuɗaɗen diyyar asara, da lalacewar muhalli, da fatan asusun zai yi aiki yadda ya kamata.

Har ma babban magatakardar MƊD Antonio Guterres ya ce taron na bana, ya zamo wani ginshiki mai muhimmanci na tabbatar da adalci.

Ya ce duk da cewa kuɗaɗen da ake fatan tarawa ba za su isa ba, tara kuɗin tamkar tabbatar da aniyar siyasa ce da za ta sake gina amincin da ya riga ya gurgunce tsakanin sassan ƙasa da ƙasa kan batun sauyin yanayi.

An amince da tattara kuɗaɗen tallafawa ƙasashen dake fuskantar barazanar sauyin yanayi a taron COP27 na bana.

Ko shakka babu a taron COP27 na bana, ƙasashe masu wadata sun fito da muhimman batutuwa da suka dace, kamar batun samar da kuɗaɗe, da tallafin ƙwarewa da ƙasashe masu tasowa ka iya cin gajiyar su, tare da fatan ƙasashe masu wadata za su yi aiki tare da sauran sassan ƙasa da ƙasa, wajen gina yanayi mai ɗorewa domin gaba.

Shirin ƙasar Sin na kafa tarihin nasara a fannin yaki da sauyin yanayi
Ƙasar Sin babbar kasa ta biyu a ƙarfin tattalin arziki, kuma ƙasa mai tasowa mafi girma a duniya, don haka fannoninta na ayyukan masana’antu da sarrafa hajoji na kan gaba a duniya.

Dalilin hakan ya sa ta zama cikin manyan ƙasashen duniya masu sukuni, dake fitar da tarin nau’o’in sinadarai da iska mai ɗumama yanayi.

Sai dai sabani wasu ƙasashe dake ƙoƙarin kawar da kai, ko gaza cika alƙawura game da magance sauyin yanayi, Sin ta yi rawar gani wajen sauke nauyin dake wuyanta, a fannin rage fitar da wadannan nau’o’in iska, da ma sanya wa’adin kaiwa ga yanayin daidaito tsakanin iskar Carbon mai dumama yanayi da take fitarwa da matakan kawar da ita.

A baya-bayan nan ma, wakilin musamman na ƙasar Sin game da sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya ƙarfafa gwiwar kasashe masu sukuni, ta hanyar yin kira gare su da su ba da gudummawa, ga cimma nasarar manufofin dake ƙunshe cikin yarjejeniyar Paris, ta hanyar kafa asusun diyyar asara, da lalacewar muhalli ƙarƙashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD ko UNFCCC, domin taimakawa ƙasashe masu tasowa, ta yadda za su shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi.

Masharhanta na ganin cewa, duba da yadda ƙasar Sin ke kan gaba wajen cin gajiya daga fasahohin daƙile sauyin yanayi, musamman fannin bunƙasa amfani da nauo’in makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa.

Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga ƙasashen Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci ya yi da ƙasashe masu tasowa za su rungumi tafiya tare da Sin a wannan fanni.

Sin na aiwatar da matakai daban-daban na karkata akala zuwa ga amfani da makamashi mai tsafta.
Ya zama wajibi a daidaita fitar da iska da sinadarai masu ɗumama yanayi da matakan kawar da mummunan tasirinsu.

A cewar Frederick Mutesa, wani ƙwararre a fannin ilimin samar da ci gaba ɗan ƙasar Zambia, ƙasar Sin ta nunawa duniya ƙwazonta a fili, wajen bunƙasa ci gaba mai ɗorewa, da raya manufofi, na daƙile ƙalubale, da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Ko shakka babu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin ƙasashen nahiyar Afirka da sauran sassan ƙasashe masu tasowa, na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya ɓangaren ƙasar Sin ke da ƙwarewa, da fasahohin bunƙasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi haɗin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.

Baya ga fannin raba fasahohi da ƙasashen Afirka, fannin samar da kuɗaɗen daƙile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin ɓangare ne da ƙasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cuɗanya tsakanin ƙasashen Afirka da Sin ƙarƙashin dandalin FOCAC, na bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da ƙasashen Afirka ke samu daga Sin, ƙarƙashin manufofin samar da ci gaba na shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”.

Tarihi ba zai manta da ci gaban da Sin ta cimma a fannin amfani da makamashi da ake iya sabuntawa ba, ta yadda ƙasar ta kafa wani misali na yadda ya kamata ƙasashe masu tasowa ya dace su yi yaki kafaɗa-da-kafaɗa da wannan ƙalubale na sauyin yanayi.

Ƙarƙashin manufofin Sin, ƙasar ta cimma manyan nasarori a fannin sarrafa makamashi da ake iya sabuntawa, inda alkaluma suka nuna yadda a shekarar 2021 kaɗai, ƙasar ta zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 380 a fannin sarrafa makamashi mai tsafta, adadin da ya haura wanda sauran ƙasashen duniya suka zuba a fannin.

A ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire ma, Sin na sahun gaba, inda ta samar da sabbin fasahohin zamani na sarrafa makamashi, tun daga na samar da lantarki daga ƙarfin ruwa, zuwa na amfani da hasken rana, da ƙarfin iska zuwa nukiliya.

Dukkanin waɗannan sassa na cikin jimillar hanyoyin samar da makamashi a ƙasar Sin.

Sin ta himmatu wajen amfani da hanyoyi daban-daban na kare gurbatar muhalli da daƙile sauyin yanayi.

Kazalika daga shekarar 2012 zuwa 2021, Sin ta samu matsakaiciyar ƙaruwar tattalin arziki da ta kai kaso 6.6 bisa dari a duk shekara, da ƙaruwar kaso 3 bisa dari na adadin makamashi da ƙasar ke amfani da shi.

Har ila yau, adadin iskar Carbon dioxide da ake fitarwa a ƙasar bisa ma’aunin tattalin arziki na GDP ya ragu da kaso 34.4 bisa ɗari, yayin da ƙasar ta yi nasarar rage ƙona makamashin Kwal da kaso mai yawa a tsakanin shekaru kusan 10.

Masu fashin baki na ganin cewa, akwai shaidu dake nuna yiwuwar ɗorewar haɗin gwiwa tsakanin Sin da sauran ƙasashe masu tasowa, musamman a fannonin sauya alƙiblar sarrafawa, da amfani da makamashi daga nau’o’in albarkatun mai, zuwa makamashi masu tsafta, da waɗanda ake iya sabunta amfani da su da ma na bola-jari.

Sai dai fa duk da hakan, akwai babban nauyi a wuyan sauran manyan ƙasashe masu arzikin masana’antu, waɗanda ke samar da ƙarin kaso mai tsoka na abubuwan dake dumama yanayi.

A shekarun baya bayan nan, ƙasar Sin na da tsare-tsare na dogon zango, dake da nufin dora ƙasar kan turbar karkata yanayin tafiyar da tattalin arzikinta, daga fannonin zuba jari kan ababen more rayuwa zuwa fannin ƙirƙire-ƙirƙire, kana daga fannonin fitar da hajoji zuwa na kyautata kasuwannin cikin gida.

Da wanzar da ci gaba ba tare da gurɓata muhalli ba. Fatan dai shi ne ɗaukacin sassan duniya za su ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe, wajen tabbatar da nasarar manufofin da aka sa gaba, a fannin dalike mummunan tasirin sauyin yanayi, da wanzar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ta yadda dukkanin bil adama zai samu zarafin yin managartacciyar rayuwa a duniya.