Buhari ya ƙaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri wacce aka fi sani da Dala ‘Inland Dry Port’ a unguwar Zawaciki, Jihar Kano.

Shugaba Buhari ya isa wajen ne da misalin ƙarfe 10:32 na safiyar Litinin tare da rakiyar wasu daga cikin ministocinsa.

Shugaban ya samu tarbar Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Sufuri, Jaji Sambo da Manajan Daraktan tashar ta Dala Inland, Ahmad Rabiu da kuma shugaban tashar Alhaji Abubakar Sahabu.

Sauran manyan baki da su ka halarci taron sun hada da Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya, NSC, Emmanuel Jime; Babban Sakatare, Ma’aikatar Sufuri, Magdalene Ajani da tsohon Babban Sakatare, NSC, Hassan Bello da sauran manyan baƙi.

By Editor