Daga BASHIR ISAH
Rahotanni daga ƙasar Pakistan sun tabbatar da aukuwar wani mummunan harin da aka kai masallaci wanda ya yi ajalin mutum 61.
Waɗanda suka mutu a harin na ranar Litinin har da jami’an tsaro, kana mutum 150 sun jikkata.
An kai harin ne a daidai lokacin jama’a suka haɗu domin gudanar da sallar Azahar a madallacin da ke hedikwatar ‘yan sandan Pakistan da ke birnin Peshawar.
Ana ci gaba da aikin ba fa agaji a inda iftila’in ya auku, wanda ginin masallacin ya tarwatse saboda ƙarfin fashewar da ta auku.
Shugaba Rundunar ‘Yan Sandan Peshawar, Mohammed Ijaz Khan ya ce, kimanin ‘yan sanda 300 zuwa 400 yawan halartar masallacin kulli yaumi.
