Ko Kanawa sun yi lale da ziyarar Buhari?

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyar aiki na kwana biyu a Jihar Kano domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ya aiwatar.

Sai dai, da alama Kanawa ba su yi ɗaukin ziyarar Buharin ba saɓanin abin da aka saba gani a baya.

Kafin ziyarar tasa, an abato Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje, ya ce, ya nemi Shugaba Buhari ya ɗage ziyarar da ya shirya yi a Kano sakamakon jama’a na cikin mawuyacin hali saboda canjin kuɗi da aka yi.

Rahotani, hotuna da ma bidiyoyi sun nuna yadda a wasu titunan jihar galibi yara kaɗai suka fito don tarbar shugaban.

Majiyarmu ta nuna ‘yan siyasar Jihar Kano sun daɗe suna ƙorafi kan jinkirin da Buhari ya yi kafin kai ziyarar jihar da ake yi wa kallon ita ce ƙarfin siyasarsa.

Wasu na ra’ayin cewa Buhari ya kai ziyara Kano a wannam lokaci ne saboda ganin zaɓe ya ƙarato.

Yayin da wasu kuma ke cewa ya yi jinkirin kai ziyarar ne saboda babu wani aiki da Gwamnatin Tarayya da za a nuna a jihar a shekaru biyu da jawan Buhari mulki.

Kimanin ‘yan sanda 8,000 aka jibge a jihar baya ga jami’an tsaron farin kaya da sojoji don ba da tsaro yayin ziyarar Buhari.