Tilas ce ta sa na fito takarar Gwamnan Sakkwato – Dakta Sifawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Yayin da manyan zaɓukan 2023 musamman ma zaɓen gwamnoni ke daɗa ƙaratowa, wani abu da ya soma ɗaukar sabon salo a siyasar Nijeriya shi ne, fitowar jama’a takarar gwamnoni a ƙananan jam’iyyun siyasa duk wasu na masu kallon ‘yan amshin shata ne kawai ta la’akari da cewa, ba su fiye yin tasiri ba  a siyasar Nijeriya wajen kafa gwamnati. Wakilin Blueprint Manhaja a Sakkwato, Aminu Alhussaini Amanawa ya zanta da ɗan takarar gwamna na jami’ar ADP, Dakta Ibrahim Mahammad Liman Sifawa, wanda ya ce tilas ce ta sa shi fitowa takarar domin canza abinda ya kira da gurbatattun shuwagabannin da suka dakusar da cigaban Sakkwato ta yanda za ta yi gogayya da takwarorinta, abinda yake alaƙantawa da zaluncin nasu. Ga dai yanda zantawarsu ta kasance da wakilin namu:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatu.

SIFAWA: Sunana Dakta Ibrahim Muhammad Liman Sifawa ɗan takarar Gwamna a ƙarƙashin Jam’iyar ADP, watau (Action Democratic party) a jihar Sokoto Insha’Allah.

Meye ya ba ka qwarin gwuiwar fitowa ita wannan takarar ta gwamnan jihar Sokoto?

To, ƙwarin gwuiwa ya samu mataki -mataki. Na farko dai ina cikin waɗanda ke da damuwa matuƙa ga halin da ƙasarmu take ciki, musamman jahar Sokoto, sannan kuma duk matsalolin da muke fuskanta za ka samu cewa kowa na da laifi, amma shugabanni su suka fi kowa, wato matsala ta shugabanci, duk abinda aka ba su, Allah ya ba mu, duk wata ni’ima da akwai ta.

Jahar Sokoto tana ma iya zama matsayin ƙasa, don akwai ƙasar da idan Allah ya so cikin ƙasashen Afirka wadda jahar Sokoto ta fi ta arziki, amma saboda babu jagoranci da nagarta sai ya zamo kullum baya muke ci, har ka ji ma an kai ga samu, mu ne da tuta ta duniya ta fatara da rashi Ubangiji Allah ya yi mana maganin wannan. To, duk ɗan adam da yake da hankali yana kuma ganin yadda al’umma suke cikin wannan halin bai damu ba, kansa kawai ya sani.

Shi dai ya samu Abinci ya samu kaza, ya yi kaza, to duk arzikin da ke gareka da ni’imar da ka ke ciki, al’umma da ka ke ciki tana cikin damuwa to aiki bai ƙare ba. Sannan aikin nan da za a yi mutane ke yin sa, mutane ke ɓarna su ne suke gyara. Wasu sun yi ɓarna, to dole ne a zo a yi gyara. To irin wannan damuwar ina da cikinta, har ya zamo muka haɗu ire-irenmu ta hanyar tattaunawa, har aka cimma matsawar dai babu hanya in ba a ɗauko wata jam’iyar ba wanda ba APC ba, ba kuma PDP ba. Saboda su suke da manyan jam’iyyu da suka gwada a wannan jahar tamu tun daga 1999 har yanzu, babu alamun cewa har yanzu za a iya samun gyara cikinsu idan dai ba wani wahayi ko abinda ya samu ba. A kan haka ne ya sanya muka ɗauko wannan jam’iyyar kuma har aka zo mataki-mataki har aka tsayar da ni ɗan takarar gwamna a wannan jam’iyyar.

To, amma kana maganar kun ɗauko wata jam’iyya ne domin ku canja salon tafiyar da su wadannan jam’iyun suka daɗe suna mulki, kana ganin hakarku za ta cimma ruwa kuwa, la’akari da daɗewa da tarihi da yawan magoya bayan da su waɗannan jam’iyyun suke da su?

Eh, ƙwarai da gaske ai kusan ma haƙar ta cimma ruwa. Domin na ɗaya dai, talakawa sun waye, waɗannan jam’iyyun da kake faɗa sun fita daga matsayin jam’iyun, wasu kamfanoni ne na waɗanda wasu ke da jari. Idan ka duba 1999 wanda duk bai da jari ciki to bai da wani abu da zai yi ba ya ciki.

Amma talakawa suke jefa musu kuri’a kuma?

Eh mana, don babu wata mafita ba, yanzu kuma an samu mafitar, wacce ita ce haƙarmu da ta kai ga ruwa. Yanzu haka da kana shiga lauyuka da birane da za ka ji har shugaban jam’iyyu akwai, kafin tamu jamiyyar ta fito. Saboda haka, da APC da PDP sun zamo wa wasu kamfanonin zuba jari, kuma talakawa sun gane. A kan haka kusan sun ajiye su gabaɗaya, wasu ba su ma da niyyar yin zaven amma dai Alhamdulillah fitowar da muka yi da manufofin da aka yi to su ne suka share hawayen al’ummar jihar Sokoto, kuma yanzu sun jajirce Insha’Allah ADP za su zaɓa kuma ita za ta kafa gwamnati.

Da akwai wani hasashe da aka yi da ke nuna  jahar Sokoto na da yawan al’umma kusan miliyan biyar a ƙiyasi. Za ku iya kiyasta naku magoya bayan za su iya kai wa nawa a cikin miliyan biyar ɗin nan idan za mu ƙaddarta?

Ai mu in banda waɗannan da  ke riƙe da muƙamai na PDP da APC ko wasu waɗanda sun riga sun saba da wauta, har idan suka ga ‘yanci gudunsa suke yi tsoronsa suke yi, ko waɗanda zuciyarsu ta mutu gabaɗaya ba su zaton Rahma da Allah kansu kaɗai suka sani, ganin su suke yi babu wani abunda zai faru, inda ake a nan ake.

Kuma waɗannan mutane ina mai tabbata maka, ‘yan cokali ne. Saboda haka, kusan ban iya bayar da alƙalami don ban son mu yi magana ta ƙarya, amma yadda nake tabbatar maka mafi yawan al’umma waɗanda ke da hankali mai saiti dai-dai, to suna goyon bayanmu. Sai dai in da labari bai kai ba, kuma muna nan muna ƙoƙari da su ji abinda muke ciki, to wannan shi ya nuna mana waɗancan jam’iyyun ba su da kowa. Domin kuwa yawan mutane shi ne kasuwa!

Ka na ta maganar kuna da magoya baya menene sirrin samar da magoya bayan da  ka ce kuna da, da akwai waɗansu abubuwa ne da  suka bambanta ku da sauran jam’iyyun ne?

Qwarai da gaske! Na farko dai, su waɗannan jam’iyun an gaji da su, sun yi an gani kowa bai more ba. Na biyu kuma, su waɗannan da ke tafiyar da abin kuma ya zama har ma al’umma gabaɗaya takaicinsu suke, saboda babu abinda suka yi musu, wanda yake dai-dai. Ban ce maka ɗaɗaiku ba, domin abinda ke gare su a kowanne gari suna da ɗan baranda guda 1 wanda shi ne madadin wannan garin, idan suka ƙare shikenan, wannan ɗan barandan in ba a yi ba takaicin shi suke ji, don ba a yi musu komai ba. Akwai waɗanda yake ‘yan barandan garin nan, amma suka amsar kuɗi ba su ma iya shiga wannan garin.

Don haka, wannan shi ne sanadi na farko. Su waɗannan jam’iyun sun dasa kuma al’umma sun gane. Na biyu, mutane suna lalube don ana cikin duhu, ina za a shiga. To mu mafitar da muka bayar ita ce, yaƙi da zalunci. Mun tabbatar wa al’umma cewa, Allah muka nufa, kuma waɗannan kalaman muna jaddadawa ne domin Allah ya ce, a yi gaskiya, da adalci, kuma Insha’Allah su za mu yi idan mun samu dama, don ba dole ba ne sai mun yi ƙarya.

Ɗaya daga cikin matsalolin da ke damun Sakkwatawa a yanzu bai wuce matsalar tsaro ba, ta ya za ku tunkari matsalar idan kun samu dama?

To, komai yana da musabbabi, kuma asalin wannan matsala shi ne, zalunci. Turawa lokacin da suka zo sun yi na’am da adalci domin a lokacin mace kan iya ɗaukar zinare tun daga nan Sokoto har Gombe a ƙasa ba wanda zai taɓa ta, saboda adalcin shuwagabannin wancan lokacin. Amma yanzu zalunci da rashin adalcin da ake yi shi ya sa Allah ya yi fushi ya bar mu da dabararmu.

Wannan matsala maganinta ba wai soja ko ɗansanda ba ne, wallahi tun da aka taɓa Allah, sai mun ɗanɗana kuɗarmu. kuma wannan ba ni na faɗa ba, Allah ya ce, duk inda zalunci ya yawaita, Allah da kansa zai sauko maku da masifa. Yanzu ɗan uwanka zai iya rufe fuska ya zo ya yi garkuwa da kai, ko maƙwabcinka ya sa a yi garkuwa da kai. A taƙaice dai, tava Allah aka yi. Ma’ana, zalunci ya yawaita shi ya sa masifu suke bin mu, saboda halin da ake ciki talaka bai ko san akwai gwamnati ba, komai ya faru da kai, sai dai ka kai ƙara wajen Ubangiji.

A da ne idan aka zalunce ka, ka kai wa hakimi, ya ɗauka ya kai wa uban ƙasa, shi kuma shugaban ƙaramar hukuma har a yi ma adalci. Amma a yanzu fa? ba wanda za ka gaya wa. Domin su kansu sarakuna sun zama ‘yan kallo.

Kenan kai yaƙi da zalunci za ka sanya a gaba?

Eh, yaƙi da zalunci shine na farko, domin duk sanda aka taɓa masu rauni, marasa gata, to wallahi ba mai samun gata. Idan muka gyara wannan, Insha’Allah za a samu mafita.

Jihar Sokoto tasha ɗaukar kambun zama jagaba ta jihohin da suka fi fama da fatara da talauci. Ta ya za ku fuskanci wannan?

Wayyo, watau abinda ɗaure kai idan ka tafi wurare da yawa, za ka ga ruwa yana gudu a ƙasa, akwai arzikin da ya wuce wannan? Amma sai ka ga rashin ƙarfafawa ta jefa mutanen cikin talauci.

Idan aka yi zaɓen nan, ba ku yi nasara ba, za ku rungumi ƙaddara?

Me zai hana? sai dai ba za mu goyi bayan wannan ɓarna ba. Kuma ba ‘yan adawa ba, sai dai za mu kasance mafita kan ɓarnar da ake.

Ku ADP kuna da kuɗin da za ku iya ba wa talakawa su zaɓe ku, la’akari da yadda wasu ke gudanar da siyasar kuɗi, duk da ya saɓa wa doka?

To, a bayyane yake ba, hukumar zave ta INEC ta haramta, amma wasu suka zo :yan kasuwa suka mayar da siyasar kasuwanci. Kuma mu so muke a koma kan turba. Kuma ka sani, mu ba mu da kuɗi, amma za mu yi ƙoƙarin canza tunanin al’umma.

Da me za ka rufe mana?

Saƙona ga al’umma shi ne, kowa ya san dai-dai. Don haka, mu yi amfani da iliminmu wajen samar da shugaban da ya fi dacewa gare mu da zai samar mana da mafita a halin da jihar mu ke ciki. Kuma Insha’Allah, za mu yi amfani da damarmu wajen daidaito tsakanin birni da ƙauye. Duk Sokoto birni xaya ne kawai, amma kuma bai jayayya da wasu jihohi.

Ka tafi Dutse sabo ne, wallahi akwai ginin da idan ka gan shi sai ka yi kallo, amma duk sakkwato birnin ɗaya ne. Ba wani ginin da Baƙauye zai kalla ya ba shi sha’awa, ba abinda ke gabansu sai rabon filaye, da yin filaza, da siyar da biskit da alawa. Don haka, muna kiranku da yin gyara, kuma ko gobe ƙiyama za mu tashi gaban Allah cewa wasu sun yi varna, mun yi ƙoƙari na yin gyara.