Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki

Daga WAKILINMU

Daraktan ayyuka na Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), Niyi Alli ne ya sanar da hakan ranar Litinin.

Sanarwar da ya fitar ta nuna tsarin lokutan da jirgin zai riƙa zirga-zirgar jagilar fansinjoji.

Sanarwar ta ce, “Ranar Talata, 31 ga Janairun 2023 jirgin zai kama aiki bisa tsari kamar haka:

KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700

AK1 zai bar Idu da ƙarfe 10.00

KA4 zai bar Rigasa da ƙarfe 13.00

AK3 zai bar Idu da ƙarfe 16.00.

“Sai dai a ranar Laraba, KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700 yayin da AK 3 zai bar Idu da ƙarfe 16.00.

“Hukumar ta nuna damuwarta kan rashin sukunin da ta jefa fasinjoji sakamakon tsaikon da jirgin ya samu,” in ji sanarwar.