Dandalin shawara: Mijina ba ya fashin kusanta ta lokacin da na ke jin al’ada

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assamu alaikum wa rahmatullahi. Hajiya Aisha ya ƙoƙari. Ya kuma fama da jama’a. Kwana da yawa. Fatan duk iyalai lafiya. Sunana…………daga nan………….. Mun ɗan yi magana da ke a shekarun baya, lokacin littafinki na ‘Soyayyar Ƙarya’, har ki ka ba ni shawarwari kan matsalata, kuma na ji daɗin su ainun, don sun fitar da ni matsalar. To yanzu ma wani abu ne ke ci min turo a ƙwarya. Wallahi mijina ne dai al’amarinsa ya fara damuna, matsala ce da ta kai kusan shekara yanzu, muna iya kwashe kusan sati uku zuwa huɗu bai damu da neman haƙƙinsa na aure ba, amma da an ce ma ki na fara jinin al’ada to fa ba fashi, duk dare sai ya kusance ni, har tambaya yake yaushe ne zai zo. Mijina na da zafi, amma akan kusanta ta lokacin al’ada idan na hana shi zai ta rarashi na, sam ba ya fushi. Rabon da ya kusance ni Ina da tsarki har na manta. Da abin ya dame ni ne, na ce, bari na sake taɓo ki, don na san zan sami mafita. Me ya kamata na yi, Hajiya Aisha.

AMSA:

Wa’alaiki salam wa rahmatullah. Alhamdu lillah. Kafin komai, ‘yar uwa za mu fara da hukuncin wannan ɗabi’a ta maigidanki a Musulunce. Aya a cikin littafi mai tsarki ta ce, “Su na tambayar ka (manzon Allah) game da jinin al’ada (wanda aka fi sani da jinin haila) ka ce mu su, ƙazanta ne, su nisanci mata a cikin jinin.”

Kusantar mace a lokacin jinin haila haramun ne, kamar yadda malaman tafsiri suka bayyana. Idan kuwa abu ya faɗa bisa hukuncin haramun, to zai bi jerin hukuncin da hadisin Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “babu ɗa’a ga abin halitta(mutum ko aljani) wurin saɓa wa mahalicci (Allah).”

Tambaya ta ta farko, shin ke da mijinki kun san da wannan hukunci? Idan kuwa kun sani, zan ce kun kasance masu babban laifi, musamman ke da ake yi wa.

Abu na farko, na san zuciyarki ko waɗanda ki ka tava gayawa wannan lamari sun tava sanar da ke akwai yiwar tsafi ne yake yi, kuma wannan xabi’a ce sharaɗin da mushrikan suka gindaya masa. Zai iya yiwa hakan, kuma zai iya yiwa ba hakan ba ne.

A ‘yan kwanakin baya da aka ba mu wani horo da ya shafi ƙwaƙwalwa, na fahimci cewa, ƙwaƙwalwa akalar ɗabi’un ɗan adam ce, kuma tana tattare da matsaloli masu yawa da alamomin su suka fi kama da sheɗana ko tsagaron son rai. Ba wai Ina ƙoƙarin danganta duk wani ashararanci da ɗan adam zai yi kan matsalar ƙwaƙwalwa ba, sai dai akwai ɗabi’u da dama da ta ke ɗaukar alhakin faruwar su.

Akwai wata matsala da ke raya maka sha’awar abin da yake abin ƙyama ko wanda mutane da dama ba sa son yin sa. Kamar misali, akwai wanda ba ya sha’awar kusantar mace ta lalama, ya fi gamsuwa idan ya yi mata fyaɗe.

Da dama daga cikin masu wannan ɗabi’a za ka tarar suna fama da matsalar ƙwaƙwalwa, idan ka cire masu yi don biyan buqatar duniya (tsafi) ko masu yi don tsananin rashin imani (‘yan ta’adda da makamantan su).

Zai iya yuwa mijin naki mijin tsafin yake yi, idan haka ne, biye masa da ki ke yi ina zai kai ki? Kuma zai iya kasancewa akwai matsalar ƙwaƙwalwa da ta ke sa shi yin wannan ɗabi’a, idan ki ka ci gaba da biye masa cutar zata ci gaba da ƙaruwa, me ki ke tunanin gaba zata sa shi ya aikata? Idan kuwa tsabagen son rai ne da yi wa sheɗan biyayya ya kai shi ga wannan, me ki ke tunanin gaba zai ma shi umurni da aikatawa?

Sau da yawa mata na da wata ɗabi’a da mafi yawan lokuta ke kai su ga halaka ko danasani. Mazajensu za su buƙaci yin wani abu da zuciyarsu ta tabbatar masu ba mai kyau ba ne, kuma zai iya cutar da su, amma sai su biye wa son rai na mazajen nasu, su aikata don mazan su ji daɗi.

Mijinki na kusantar ki kawai a lokacin da ki ke al’ada, idan kin gama ya gama da ke, kuma wannan abu ya kwana biyu yana faruwa, wanda hakan ya ba ki lokaci mai tsayi na yin nazari kan lamarin, tambayata gare ki ‘yar’uwa, shin kin tava tunanin illar haka ga lafiyarki?

Kuma kina da tabbacin idan wata matsala ta same ki, zai jure zama da ke? Ko wani vangare na zuciyarki na sanar da ke yiwar ya bar ki da matsalar ya tsallaka ya yi wurin wata? Idan akwai yiwar ya guje ki, menene fa’idar yi masa sadaukarwar?

Za mu ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *