Har yanzu dai Nijeriya ita ce jagaba wajen samar da fetur a Afirka – OPEC

Daga AMINA YUSUF ALI

Duk da qalubale da matsalolin da ta sha fuskanta, ya zuwa ƙarshen shekarar 2022, Nijeriya ta kasance ita ce kan gaba wajen samar da man fetur a Afirka.

Wannan lafazin ya fito ne da yawun Ƙungiyar ƙasashen masu samar da man fetur a Duniya (OPEC). OPEC ta bayyana cewa, Nijeriya ta ƙarƙare shekarar 2022 a matsayin qasar da ta fi kowacce samar da man fetur a Nahiyar Afirka.

A cewar OPEC, Nijeriya a watan Disamba na shekarar bara ta samu ƙarin kaso 4% na man fetur ɗin da take samarwa. Wato gwari-gwari ta tashi daga samar da gangan miliyan 1.186 kowacce rana a cikin watan Nuwamban shekarar, ta koma samar da ganga miliyan 1.235 a kowacce rana. Haka a matsakaicin lissafin shekara-shekara, shi ma an ga sauyi matuƙa.

OPEC ta saki wannan rahoto ne a cikin Rahotonsa na wata-wata na kasuwar man fetur (MOMR) na watan Janairu 2023 wanda ya wallafa a shafinsa na yanar gizo.

Kodayake, a shekarar 2022, kasuwar man fetur ɗin Nijeriya ta faɗi warwas a dalilin satar hanya da ake yi masa, a taqaice ma dai NNPC ya ba da rahoton cewa, a dalili haka sun rasa kaso 95 na man da suke samarwa a Bonny Terminal, a jihar Ribas.

Wannan ya sa wasu ƙasashen Afirka suka samu damar cin kare su ba babban a kasuwar man fetur. Har ma suka sha kan qasar Nijeriya.

Duk da haka, rahoton OPEC ya rawaito cewa, a cikin watan Disamban bara Nijeriya ta samu nasarar doke babbar abokiyar hamayyarta, ƙasar Angola, wacce take samar da gangar mai 1.088 a kullum.

Yayin da ƙasar Equatorial Guinea kuma ta ɗau lambar ƙarshe don takan samar da gangar man fetur 54,000 kowacce rana.

Amma duk da haka fa, rahoton na OPEC ya bayyana cewa, har yanzu fa Nijeriya ba ta yi wata rawar gani ba.

Domin za ta iya samar da fin haka na man fetur. Wato idan ta ƙoƙarta abinda ya kamata ta iya sanarwar zai iya kai wa ganga 1.8 a kowacce rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *