Tsoffin takardun Naira: Majalisa ba ta aminta da ƙarin wa’adin da CBN ya yi ba

Daga WAKILINMU

Majalisar Wakilai ta ce ba ta aminta da tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar Naira da ƙarin kwanaki 10 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi ba.

Kwamitin Majalisar mai ruwa da tsaki kan sha’anin sauya fasalin wasu takardun Naira, ya ce dole CBN ya yi abin da ya kamata kamar yadda yake ƙunshe a sassa na 20, 3, 4 da kuma 5 na Dokar Babban Bankin Ƙasar.

A cewar Kwamitin, “Tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da kwana 10 ba shi ne mafita ba.

“A matsayinmu na Kwamitin Majalisa ba za mu amince da wani abu sabanin abin da sassa na 20, 3, 4 da kuma 5 na Dokar CBN suka nuna ba,” in ji shugaban kwamitin, Honorabul Alhassan Ado Doguwa.

Da fari dai CBN ya ƙayyade 31 ga Janairu a matsayin lokacin da za a daina karɓar tsoffin takardun N200, N500 da kuma N1000.

Sai dai kuma a ranar Lahadi an ambato Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da izinin tsaiwata wa’adin zuwa 10 ga Fabrairu.

A martaninsa dangane da tsawaita wa’adin, kwamitin ta bakin shugabansa Honorabul Alhassan Ado Doguwa, ya ce bai yarda da ƙarin ba.

Ya ce dole CBN ya koma ya yi biyayya ga tanade-tanden da ke ƙunshe a sassa na 20 da 3 da 4 da kuma 5 na Dokar CBN.

A cewar Doguwa, “Najeriya ƙasa ce mai tasowa don haka wajibi ne a kiyaye tsare-tsaren da doka ta shimfiɗa.

“Muna ganin akwai wasu take-take da wannan tsari na sauya takardun naira na yi wa Babban Zaɓen da ke tafe zagon ƙasa.

“Sanin kowa ne cewa ta hanyar fitar da tsabar kuɗaɗe ake biyan alawus-alawus ɗin jami’an tsaro da ke jibintar lamarin gudanar da zaɓe a kasar nan musamman a matakin jiha.

“Kuma Majalisar za ta rattaba hannu kan izinin kamo Gwamnan CBN don tilasta masa bayyana a gabanta,” in ji shi.

Idan ba a manta ba, a zamanta na Talatar da ta gabata, Majalisar ta kafa kwamitin biyo bayan ƙorafe-ƙorafen ‘yan ƙasa kan matakin canjin kuɗi da CBN ya ɗauka.