Buhari ya tafi Habasha ana tsaka da balahirar canjin kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha domin halartar taron zaman lafiya na Mungiyar Tarayyar Afrika (AU) karo na 36.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce, Buhari ya bar Nijeriya ne a Alhamis, 16 ga Fabrairu, 2023.

Fadar Shugaban Ƙasar ta kuma ce, a yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai halarci taron tattaunawa kan matsaloli da ke addabar ƙasashen yammacin Afirka, tare da shugabannin ƙasashen.

Zai kuma halarcin zaman shugabannin ƙasashen ECOWAS, kuma zai gabatar da jawabai, kafin daga bisani ya dawo Abuja ranar Litinin.

Buhari kai ziyarar aikin ne sa’o’i kaɗan bayan jawabinsa ga ’yan Nijeriya kan canja kuɗi, inda ya ƙara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira 200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Ya kuma amince a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200 kafaɗa-da-kafaɗa da sabbin Naira 200, 500 da 1,000 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu da tsoffin 200 za su daina aiki.

A cewarsa, zai ci gaba da lura da yadda tsarin sauyin kuɗin ke tafiya domin kada ya jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci na babu gaira, babu dalili.

Ya bayyana cewa, CBN zai ci gaba da aiki domin tabbatar da ’yan Nijeriya na samun tsabar kuɗi ta hannun bankuna.

A halin da ake ciki, wasu gwamnoni sun maka CBN da Gwamnatin Tarayya a Kotun Ƙoli kan sauyin kuɗin.

Kotun ta sanya 22 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari’a bayan ta ɗage lokacin aiwatar da wa’adin CBN na daina amfani da tsoffin kuɗin ranar 10 ga watan Fabrairu.

By Editor