Da ɗumi-ɗumi: CBN ya umarci bankuna su karɓi N500 da N1000

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara karɓar tsoffin takardun N500 da N1,000 daga hannun jama’a nan take.

Sai dai, CBN ya sharɗanta cewa Naira 500,000 ita ce mafi girman abin da bankunan za su karɓa amma ban da abin da ya haura haka.

Majiyarmu ta ce CBN ya ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa jama’a wahalar zuwa rassan CBN a faɗin ƙasa don mayar da tsofaffin kuɗin.

Wani jami’in CBN ya ce, “Ku tafi bankunanku, amma ku tabbatar kun cike fom kafin ku tafi. Ku je da kebaɓɓun lamɓoɓin da kuka samu.

“Bankuna za su karɓa, amma idan kuɗin ya haura N500,000 dole sai an dangana da CBN,” in ji shi.

Tun farko, CBN ya buɗe wani shafinsa na intanet don amfanin masu buƙatar miƙa masa tsoffin kuɗi inda za su shigar da bayanansu su kuma samu wasu keɓaɓɓun lambobin musmman.

A ranar Alhamis Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ba da umarnin bankuna su fito da tsohuwar N200 su ci gaba da raba wa jama’a biyo bayan tsawaita amfani da ita da Shugaba Buhari ya yi.

Kana ya buƙaci duk mai tsoffin N500 da N1000 a kai wa CBN.