CBN ya ƙaryata bai wa bankuna damar karɓar tsoffin N500 da N1000

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya ya ce hankalinsa ya kai kan wasu saƙonnin ƙarya da ake yaɗawa inda aka ce bankin ya bai wa sauran bankuna damar karɓar tsoffin takardun N500 da N1000.

Cikin sanrwar manema labarai da ya fitar da yammacin Juma’a, CBN ya ce wannan batu ba gaskiya ba ne.

Domin kwaranye wa mutane kokwanto, CBN ya ce N200 kaɗai aka yarda a ci gaba da amfani da ita kamar yadda Shugaban Ƙasa ya sanar a jawabinsa da ya gabatar ranar Alhamis, 16 ga Fabrairu.

Kuma ƙarin wa’adin da aka yi wa N200 zai yi aiki ne na tsawon kwana 60, wato zuwa 10 ga Afrilu, 2023.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Darakta na sashen sadarwa, Osita Nwanisobi, ta ce “Jama’a su yi watsi da duk wani bayani a kan wannan batu wanda asali ba daga CBN ya fito ba.”

Sanarwar ta shawsrci ‘yan jarida da su riƙa tantance labari kafin su yaɗa.

Idan ba a manta ba, a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasa a ranar Alhamis aka jiyo Shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar N200 da kwana 60, tare da cewa a maida tsoffin N500 da N1000 CBN saboda a cewarsa, aikinsu ya ƙare.