APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamnanta a Adamawa

Daga BASHIR ISAH

Shugabancin Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa ta dakatar da mai yi wa jam’iyyar takarar gwamna a jihar, Sanata Aishatu Ahmed Dahiru Modibbo (Binani), daga jam’iyyar.

Wasiƙar dakatarwar wadda ta samu sa hannun jami’an jam’iyyar 21, ta nuna an ɗauki matakin dakatar da Binani na tsawon wata shida daga jam’iyyar ne saboda zargin rashin biyayya ga kotu da ake yi mata.

Kazalika, shugabannin jam’iyyar sun zargi Binani da haddasa ɓangaranci da rarraban kan mambobin jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ‘yan kwanaki kafin zaɓen gwamnoni a faɗin ƙasa.

Ga cikakken bayanin da wasiƙar ta ƙunsa:

Wasiƙar dakatar da Sanata Binani